Binta Ola Ta Rasu Bayan Ta Kammala Shirye-Shiryen Gudanar Da Mauludin Annabi SAW.

An yi jana’izar dattijuwar fina-finan Kannywood Binta Ola a birnin Katsina, wadda Allah ya yi wa rasuwa a daren Laraba bayan gajeriyar jinya.

 

Jaruma Hajiya Binta Ola ta rasu jim bayan ta kammala Aiyukan Maulidin Annabi (SAW).

 

Hajiya Binta ta Rasu da misalin karfe 3:00 na dare, bayan Kammala Ayyukan Gudanar Bikin Mauludin Manzon Allah SAW da zata gabatar da Safiya yau Larabar.

 

Anyi sallar jana’izan ta da misalin karfe 10:00 Na safiyar ranar a gidan ta Dake Sabuwar Unguwa kofar kaura santa Mai kalon chake suffer market Jihar Katsina.

 

Bayanan da BBC ta samu sun ce dattijuwar ta kammala shirye-shiryen gudanar da bikin Maulidi a safiyar Laraba, amma sai ta kamu da rashin lafiya da tsakar dare kuma ta rasu.

 

Binta na cikin mutanen da suka gudanar da wasannin kwaikwayo na daɓe a rediyo tun kafin fina-finan zamani na Kannywood.

 

Sai dai danginta ba su da tabbas game da shekarun haihuwarta.

 

Allah ya jikan ta da rahma ya gafarta mata, Allah ya yafe mata kura kuran ta. Amiiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button