Budeddiyar Wasika Zuwa Ga Yan’uwa Tijjanawa Masu Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Na Zamani

BUDEDDIYAR SHAWARA ZUWA GA YAN CIKIN GIDA MASU GIRMA (SADATU MASU TA’AMMALI DA MEDIA).

 

•Daga dan Karamin Almajirinku.

 

Kiyayya, gaba da kuma jifan juna da muggan kalamai na zagi, na daga cututtukan zuciya da asibittocin gyaran zuciya (Dariku) ke jinyar ma’abotansa su samar musu magani da waraka, kenan duk wanda ya kasance ma’abocin bin tafarkin daya daga wadannan Dariku, to ya kamata ace tsarin rayuwarsa ta bambanta da ta sauran al’umma da basu rabauta da kasamcewa a layinsu ba.

 

Idan kaga likita ya daura maras lafiya akan wani magani, kuma ya zamto ciwon yaki warkewa, to lallaine akwai matsala a dayan uku:-.

 

1- Ko maganin bai dai-dai da kalar cutar ba.

2- Ko kuma majinyacin baya kiyaye ka’idar shan maganin

3- Ko kuma cutar tayi tsanani tafi karfin jin magani.

 

• Ni da kai mun sani, abinda Dariku suka ginu akai, sune dai wadannan magungunan da ALLAH da kansa ya bayar a matsayin sune suke samarwa zuciya waraka daga dukkanin cututtuka, wato a fadinsa a Suratul Ra’adi aya ta 28

 

الذين آمنوا وتطمئن قلوبهم بذكر الله ألا بذكر الله تطمئن القلوب

 

Ma’ana : Sune wadanda sukayi Imani, kuma zukatansu ke samun nutsuwa da ambaton ALLAH, lallaine da ambaton ALLAH zukata ke samun nutsuwa.

 

Sayyadina Abu Darda ya ruwaito cewa :

 

إن لكل شيء جلاء, وإن جلاء القلوب ذكر الله عز وجل

 

Ma’ana: Lallaine a tare da kowane abu akwai magogi, magogin zuciya shine ambaton ALLAH mai girma da daukaka.

 

Kuma ni da kai mun sani, gyaruwar wannan zuciyar da Asibittin Sufanci ke jinya shine ke haifar da gyaruwar sauran gabbai, ya zamto an guji cutar da juna da harasa da kuma hannaye wajen furta muggan kalamai, ko kuma aikata munanan ayyuka wanda hakan shine ke sawa a zamo mafiya alkairin Musulmi. (المسلم من سلم الناس من لسانه ويده )

 

Kamar dai yadda yazo a hadisin Annu’uman Bin Bashir (R.T.A) daga MANZON ALLAH (S.A.W).

 

ألا وإن في الجسد مضغة إذا صلحت صلح الجسد كله، وإذا فسدت فسد الجسد كله، ألا وهي القلب

 

Ma’ana : Ku saurara, lallaine a cikin jiki akwai wata tsoka, wacce idan ta gyaru, to dukkan jiki ya gyaru, idan kuwa ta lalace to dukkan jiki ya lalace, ku saurara, itace Zuciya.

 

√ Kaga kenan maganin da Likitocin Zuciya (Shehunnai) suka daura akai (Zikirin ALLAH) yayi dai-dai da cutar, to kenan matsalar a ina take tunda bamu rabu da ciwon ba…?

 

• Mai yiwuwa muna lazimtar Azkaran amma sam bama kiyaye ladubban yinsu, bama yinsu da tadabburi, sai ya zamto Misalinmu kamar Misalin Jami’in da aka samar dashi domin yakar rashawa da cin hanci, amma shi yafi kowa karba.

 

√ Eh lallai hasashen zai iya zama haka.

 

• Amma lallai duk yadda cututtukan zukatanmu suka kai ga gawurta, basu kai ga maganin da yazo daga ALLAH ba, kawai dai matsalar daga mu take , saboda haka sai mu nemi hanyar kawo gyara.

 

Hakan kuwa zai yiwune a lokacin da mukasan su waye mu, me ya hadamu, ina muka dosa, me girman falalar tafarkin da muke kai, wanne hatsari munanta mu’amalar ma’abotansa yake, me hakkin juna akan junansu da sauransu.

 

ALLAH YA BAMU SABATI DA ISTIQAMA, YA AZURTAMU DA IKHLASI AMIIN

 

DAGA: MUHAMMAD USMAN GASHUA

Share

Back to top button