CETON ANNABIN RAHAMA (ANNABI MUHAMMADU SAW).
CETON ANNABIN RAHAMA ﷺ
Kuzo kuji yadda Ceton Ma’aiki yake, Kuma ku kalli yadda soyayyar Sahabbai take agareshi.. Ku kalli yadda hankalinsu ke tashi idan sun ga bacin ransa.. (A KARANTA DA NUTSUWA).
_Hadisi daga Jabir ‘dan Abdullahi Al-Ansariy (rta) yace :_
“Iyalan gidan Annabi Muhammadu ﷺ sun kasance suna da wata Baiwa wacce take hidimta musu, ana kiranta da suna Bareerah (radhiyallahu anha) .
Wani mutum ya hadu da ita (bata lullube kanta ba) sai yace mata “Ya ke Bareerah! Ki lullube gashinki domin kuwa Annabi Muhammadu ﷺ ma ba zai amfanar miki da komai awajen Allah ba”. (irin maganar da wasu sukan fa’da a yanzu da sunan wai karantar da ilimi).
Ita kuwa Bareerah sai taje ta gaya wa Manzon Allah ﷺ abinda wannan mutumin ya fa’da. Sai ga Annabi ﷺ ya fito yana jan kwarjallensa, fuskarsa tayi Ja!.
Mu kuwa Jama’ar Mutanen Madeenah mukan fahimci cewa Annabi (saww) yana cikin fushi idan muka ga yana jan kwarjallensa, kuma fuskarsa tayi ja.
Don haka sai muka dauko Makamai (Kayan Yaqi) sannan muka taho muka ce masa _”Ya Ma’aikin Allah, yi mana umurnin duk abinda kaso. Muna rantsuwa da Ubangijin nan da ya aikoka da gaskiya amatsayin Annabi, da zaka Umurcemu cewa mu kashe iyayenmu Mata da Maza da kuma ‘Ya’yanmu, Wallahi da sai mun zartar da duk abinda kace muyi musu”.
Annabi ﷺ bai ce komai ba, Har sai da ya hau kan Mimbari, Yayi ma Allah godiya da kuma Kirari agareshi sannan yace ma jama’a : *”SHIN NI WANENE?”.
Sai muka ce _”Kai Manzon Allah ne ﷺ”._
Sai yace “EH HAKA NE. AMMA DAI WANENE NI?”.
Sai muka ce _”Kai ne Muhammadu ﷺ ‘dan Abdullahi ‘dan Abdul Muttalibi ‘dan Hashim ‘dan Abdu Manaf”._
Sai yace “NINE SHUGABAN (DUKKAN) ‘YA’YAN ADAM, BABU ALFAHARI. KUMA NINE FARKON WANDA QASA ZATA TSAGE GARESHI (YAYIN FITA DAGA QABARI) ARANAR ALQIYAMAH, BAN FA’DA DON ALFAHARI BA”.
“KUMA (NINE SHIGABAN KOWA) ACIKIN INUWAR ALLAH MAI RAHAMA ARANAR ALKIYAMAH, RANAR DA BABU WATA INUWA SAI ITA, BAN FA’DA DON ALFAHARI BA”.
“MAI YASA WASU MUTANE SUKE CEWA WAI ZUMUNCINA BA ZAI YI AMFANI BA?!.
“BARI DAI (ZATA YI AMFANI) HAR SAI TA HADA DA MUTANEN JUBA’U DA HAKAM (WASU QABILU NE MASU YAWAN MUTANE AYANKIN QASAR YEMEN).”
“WALLAHI NI ZANYI CETO, INYI TA YIN CHETO HAR SAI WADANDA NA CECESU MA SUNYI CHETO, SUNYI CHETO. HAR SAI SHAITAN MA YA RIKA LEKOWA YANA KWADAYIN SAMUN CETON”.
_Aduba Musnadu Ahmad, juzu’i na 1 shafi na 281._
Gaskiyar Sayyiduna Hassanu bn Thabit (ra) da yake yabonsa acikin shahararriyar waqarsa, yace :
_*”Da hasken fuskarsa ake shayar da giza-gizai (na ruwa). Shi mai daukar nauyin marayu ne, kuma gatan Mata marassa gata ne.*_
_*”Matattu daga Iyalan gidan Hashimu zasu fake dashi, Hakika su awajensa suna cikin ni’ima da fifiko”.*_
Wannan fa shine Annabi Muhammadu ﷺ Chetonsa ba zai tsaya akan Quraishawa ka’dai ba. Har da sauran Qabeelun Larabawa, kai har ma dangin nesa-nesa, kamar mutanen Yemen.
Wadanda ya chechesu ma sai sunyi cheto, sunyi cheto.. Saboda tsantsar yawan wadanda zai cheta, har sai shaitan ma yayi tsammanin ko zai samu shiga!!!
ALLAHU AKBAR! ALLAHU AKBAR!! ALLAHU AKBAR!!!.
*Wannan sako ne daga Zauren Fiqhu Whatsapp (21-04-2017). 07064213990 08157968686.*