Cikakken Rahoton Yadda Aka Gudanar Da Hudubar Juma’a Don Murnan Mauludi A Haramin Madinatul Munawwara Dake Kasar Saudi Arabia.
CIKEKKIYAR FASSARAR KHUTABAR JUMA’AR JIYA ( 07/10/2022) DA AKA GABATAR A MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم).
قال الشيخ أحمد بن طالب، إمام وخطيب المسجد النبوي الشريف، إن أحداً من الناس مهما علا فضله واتسع علمه وكمل عقله لا يستطيع أن يحيط بمحاسن رسول الله صلى الله عليه وسلم ولا يستقصي أنواع كماله وألوان جماله صلى الله عليه وسلم-
Ma’ana: Sheikh Ahmed Bin Talib, limami kuma mai gabatar da khudba a Masallacin MANZON ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallama) ya ce: mutum komai girman darajarsa da iliminsa da kamalarsa ba ya iya (iyakance) fahimtar falalar MANZON ALLAH (S.A.W) Sallallahu Alaihi Wasallama. kada ka bincika nau’ikan kamalarsa da siffofin kyawunsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Tunani bazai kai ga riska ba).
محاسن رسول الله
وأضاف ” بن طالب” خلال خطبة الجمعة اليوم من المسجد النبوي بالمدينة المنورة: بل كلهم عاجز عن التعبير عن تلك المعاني المحمدية والصفات المصطفية ، فالله تولى إقراءه فقال له سبحانه :اقرأ باسم ربك الذي خلق ، وحفظ له ما أقرأه فقال : سنقرئك فلا تنسى ، وتولى تعليمه فقال ( لاَ تُحَرِّكْ بِهِ لِسَانَكَ لِتَعْجَلَ بِهِ إِنَّ عَلَيْنَا جَمْعَهُ وَقُرْآنَهُ فَإِذَا قَرَأْنَاهُ فاتبع قُرْآنَهُ ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا بَيَانَهُ
FALALAR MANZON ALLAH (S.A.W).
Ma’ana: Kuma ‘Ibn Talib” ya kara da cewa yayin hudubar Juma’a ta yau daga Masallacin ANNABI da ke Madina cewa: Lallai dukkansu masana (Ajizaine) ba su da ikon bayyana wadannan ma’anoni na Muhammadiyya da zababbun halaye, ALLAH mai girma da daukaka yace “Kayi Karatu” sannan ALLAH mai tsarki yace dashi ” Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.” sannan ya kiyaye masa abinda ya karanta ” Da sannu zamu karanta maka, kuma bazaka manta ba” sannan ya jibanci koyar dashi da fadinsa “Kada kayi gaggawar motsa harshenka (Dan bitar wahayi domin kiyayewa domin ya zama wajibi a kanmu mu tattara shi “Kur’ani” mu karanta shi.).
وأوضح أن الله عزوجل أمر العباد باتباع نبيه محمد صلى الله عليه وسلم وجعل أتباعه آية محبتهم لله ورسوله لقوله عزوجل ( قُلْ إِن كُنتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ قُلْ أَطِيعُوا اللَّهَ وَالرَّسُولَ فَإِن تَوَلَّوْا فَإِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ الْكَافِرِينَ) ، وذلك باتباع أقواله وأفعاله وأحواله والتعرف على سجاياه الكريمة وأخلاقه العظيمة ليتأسى به ويتبع ولا يخالف عن أمره ولا يبتدع .
Ma’ana :- Kuma Ya bayyana cewa Allah Ta’ala ya umurci bayi da suyi biyayya ga Annabinsa Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama, kuma ya sanya “Biyayya gareshi” alama ce ta son Allah da son Manzonsa, saboda fadinSa Madaukaki ” Ka ce idan kun kasance kuna son ALLAH to ku bini, sai ALLAH ya kaunaceku, sannan ya gafarta muku zunubanku, ALLAH mai gafarane, kuma mai jinkai, kace ” Kuyi da’a ga ALLAH, kuma ku yi da’a ga MANZON ALLAH, Idan kuka juya baya, to ALLAH baya son kafircewa” da Kuma ta hanyar bin maganganunsa da ayyukansa da umarninsa da sanin halayensa madaukaka da dabi’unsa masu girma, domin a yi koyi da su, da bin su da kuma barin sa6a wa umurninsa da kuma barin bidi’a.
حب النبي
وأفاد بأن حب الصحابة رضوان الله عليهم لنبيهم يحملهم على تتبع عاداته صلى الله عليه وسلم فضلاً عن غيرها، منوهًا بأن حب النبي صلى الله عليه وسلم يجب أن يفوق حب النفس والآباء والأبناء والأزواج والعشيرة والتجارة والأموال وأن أسباب المحبة ترجع إلى أنواع الجمال والكمال والنوال التي اجتمعت في مجمع صفات الكمال ومحاسن الخصال صلى الله عليه وسلم .
SOYAYYAR MANZON ALLAH (S.A.W).
Ma’ana: Kuma (Imam) ya kara da cewa, son Sahabbai, Allah Ya yardar ALLAH ta tabbata agaresu da Annabinsu, yana umartarsu da bin koyarwarsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da bin ababen wajibai da sauran su, (imam) ya kara nuni fa cewa cewa son Annabi tsira da amincin ALLAH su kara tabbata a gare shi wajibine, Lura da cewa son Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya wuce son kai (Rai), uba, diya, miji, dangi, ciniki da kuma dukiya, Da kuma kasancewar dalilan soyayya saboda nau’ukan kyau da kamala da falala da aka taru a cikin hadaddiyar sifofin kamala da falalolin siffofi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
وأكد أن الله خلق نبينا محمداً صلى الله عليه وسلم في أجمل صورة بشرية وأكمل خلقة آدمية وأجمع كلمة واصفة أنه لم يرد له مثيل سابق ولا نظير لاحق فقد كان أحسن الناس خَلقاً وخُلقاً ، فلم يرد شيء قط قبله ولا بعده أحسن منه ولا مثله صلى الله عليه وسلم فهو أجود الناس صدراً وأصدقهم لهجة وألينهم عريكة وأكرمهم عشرة .
MA’ANA :Kuma Ya jaddada cewa, Allah ya halicci Annabinmu Muhammadu Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam a cikin mafi kyawun surar mutum kuma mafi cikar halittar mutum, ya kuma hada wata kalma da ke bayyana cewa ba shi da wani misali cikin wadanda suka gabata ko makamancinsa, domin shi ya kasance mafificin mutane a dabi’u da halaye, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fi kowa kyauta, mafi ikhlasi a cikin yin zance, mafi taushin su baki daya, kuma ya fi kowa kyauta daga cikinsu (Sau ninki) goma.
واستطرد: معدداً صفاته عليه الصلاة والسلام الخلقية ، منوهًا بأن من صفاته أنه أفصح الناس لساناً وأوضحهم بياناً وإذا وعض أثر في قلوب السامعين وطيب نفوسهم حتى إنهم لتذرف دموعهم وترق وتخشع قلوبهم وهو أوسع الناس علماً وأعظمهم فهماً وأعرف الخلق بالله ، كما كان أشد الناس لطفاً وما سأله سائل قط إلا أصغى إليه فلا ينصرف حتى ينصرف السائل ، عظيم الحلم ، وأحسن الناس وأجودهم ، رحيماً بأهله والصبيان والأيتام ( وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلا رَحْمَةً لِلْعَالَمِينَ).
MA’ANA: Kuma (Imam) ya ci gaba da zayyana sifofinsa na kyawawan halaye, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana mai nuni da cewa daga cikin sifofinsa shi ne cewa: shi ne ya fi kowa iya wassafa bayani a cikin harshe kuma ya fi kowa kwarewa a cikinsu, kuma idan yana zance yana shafar zukatan mutane masu saurare, da kyautata ruhinsu, suna zubar da hawaye da tausasawa a zukatansu kuma suna masu kaskantar da kai, kuma shi ne mafi sanin mutane, mafi girmansu a cikin fahimta, kuma mafi sanin halitta a wurin Alllah . ya kasance mafi alheri da tausasawa a cikin mutane, mabukaci bai taba tambayarsa ba tare da ya saurareshi ba, don haka ba ya fita har sai mabukaci ya fita, babban mai tausayawa, mafi alherin mutane, mai jinkai ga iyalansa da yara kanana da marayu ALLAH yace (Kuma ba Mu aike ka ba face domin rahama ga talikai).
- MUNA ROKON ALLAH YA KARBA MANA ABINDA YAYI DAI-DAI YA BAMU LADANSA, KUSKUREN ALKALAMI KUMA YA GAFARTA MANA, YA BARMU DA KAUNAR MANZON ALLAH (S.A.W). AMIIN
Daga Muhammad Usman Gashua.