Cikakken Tarihin Maulana Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al Hussaini Maiduguri.

Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA

 

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da littattafai (400) na addinin Musulunci da hannunsa.

 

Malamin, wadda jigo ne a ɗarikar Tijjaniyya a halin yanzu shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Fatawa da Al’amuran Musulunci a Najeriya (NSCIA).

 

Malamin ya kasance ɗan ƙabilar Shuwa Arab, kuma ya yi karatu a wurare da dama da suka haɗa da; Makka, da Madina, da Masar, da Pakistan, da Iran, Senegal da sauran su, a wajen manyan malaman Musulunci, ciki har da babban makarancin Al-kur’anin nan Mahmoud Khalilul Khusari, a Masar.

 

An haifi Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini, CON, a daren ranar Asabar, 12 ga Mayu, 1938, a Aredibe, wani ƙauye kusa da Dikwa a Jihar Borno, da ke Arewa maso gabashin Najeriya.

 

Mahaifinsa, Sheikh Muhammad Al-Salih bin Yunus Al-Nawy, shahararren malamin addinin musulunci ne da ya yi fice a fagen ilimin addinin musulunci.

 

Mahaifiyarsa Fatima bint Sheikhh Muhammad Al-Bashir Al-Hussaini, mace ce mai yawan karamci da tsoron Allah (SWT), sannan ta kasance abar girmamawa ga kowa a cikin al’umma.

 

Ta kasance mai ladabtarwa mai kuma tsananin sha’awar ilimi. Da yake mijinta ya rasu sa’ad da ɗansu yake ɗan shekara bakwai kawai, ta karɓi horonsa har ya girma.

 

Babu shakka ita ce ta kasance mafi girman tasiri a rayuwarsa, da ta sa a yau Sheikh Ibrahim Saleh ya zama babban malami a duniya.

 

Misali, ta taɓa ƙin amincewa da shawararsa ta yin watsi da neman ilimi maimakon cinikin dabbobi, lokacin ya na ɗan shekaru goma sha biyar kacal.

 

Shakka babu, ta taka rawar gani wajen tabbatar da Sheikh Ibrahim Saleh bisa gwadabe madaidaiciya.

 

Sheikh Ibrahim Saleh, ya fara koyon Al-Kur’ani mai girma tun ya na ɗan ƙaramin yaro, in da koyaushe yake kasancewa tare da mahaifinsa, wadda ya kasance mafi yawan dararen sa ya na gabatar da sallar nafila (nawafil).

 

Wannan ne ya sa ya fara haddace ayoyin Al-Kur’ani tun kafin ya shiga makaranta gadan-gadan. Sau da dama, ɗaliban da ke karatu a wurin mahaifinsa na yawan mamakin irin ƙoƙarinsa da basirarsa sakamakon yadda yake cin su gyara a karatu duk da sun sha gaban sa.

 

Ya kuma fara karatunsa a makarantar mahaifinsa, ɗaya daga cikin shahararriyar makarantun islamiyya a Borno a lokacin.

 

Daga shekarun 1944 zuwa 1964, ne lokacin da Sheikh Ibrahim Saleh ya yi gwagwarmayar ganin ya yi tasiri a fagagen karatun Al-kur’ani da ilimin addini, da kuma sauran ɓangarorin ilimi da suka haɗa da kimiyyar lissafi, da falsafa da balagar harshe, da sauran wasu littattafai.

 

Bincikensa na neman ƙwarewa a ilimin Al-kur’ani ya fara ne a gida, wadda daga baya ya koma zuwa wasu fitattun cibiyoyin ilimi waɗanda aka fi sani da “Tsangayu” a Maiduguri da kewaye.

 

Ba da daɗewa ba shahararsa ta ɗaukaka a fannin karatun Al-kur’ani a duk wuraren da ya yi zamansa don neman ilimi, kamar: Tarmuwa, Gulumba, Gide, Maishumari da kuma Maiduguri.

 

Ya kasance mai sauƙin sha’ani, har ma ga malamai wadda ya haɗu da su a karon farko, sakamakon kyawawan ɗabi’unsa, ladabi da biyayya, da zurfin karatunsa da kuma saninsa a cikin karatun Al-kur’ani.

 

Akwai malamai da dama da suka yaba da ƙoƙarin Sheikh Ibrahim Saleh, tun ya na ƙaramin yaro kuma a matsayin ɗalibi, tare da yi masa kyakkyawar fahimta da cicciɗa shi domin kai wa ga tudun tsira a lokacin da yake tasowa a matsayin ɗalibi.

 

Akwai irin su; Sheikh Muhammadul Habib jikan Sheikh Ahmad Al-Tijjani (Abul Abbas) a ziyarar da ya kawo Maiduguri daga Aljeriya, Sheikh Muhammad Mustafa Alawi, Sheikh Al-kadi Lari Abani, Sheikh Mustafa Birshi, Sheikh Ahmad Ali Abulfathi, Sheikh Gibrima Dagira, Sheikh Tijjani Usman, Sheikh Abubakar Atiku da wasu da dama.

 

Sheikh Ibrahim Saleh, ya shafe shekaru 20 ya na neman ilimi a matsayinsa na ɗalibi, kuma ya koyi kusan dukkan karatunsa a Najeriya, amma ba hakan ke nufin duka malamansa ƴan Najeriya ba ne.

 

Ya kuma karanci harshen turanci a birnin Landan.

 

Karatun Sheikh Ibrahim Saleh, ya fi ƙarfi a ɓangaren Hadisai da Usulul Fiƙihu da Ilmul Kalam, da kuma Tafsiri. Misali, duk wata aya daga cikin Al-kur’ani idan aka ambato ta, malamin zai iya faɗin idan ta na da alaƙa da wani hadisi a tattare da ita. Malamin ya kuma yi nisa ƙwarai a karatun Tauhidi da Fiƙihu.

 

Wasu daga cikin malamansa su ne; Sheikh Al-Qadi Abanj Borno, da Sheikh Abubakar al-Waziri Borno, da Sheikh Adam al-Mahrusa Borno, da Sheikh Ahmad Abulfathi, da Sheikh Tijjani Usman (Zangon Barebari), da Sheikh Abubakar Atiku Sanka Kano, da Sheikh Muhammad al-Arabi bin Kubbani, da Sheikh Abubakar al-Kashnawiy, da Sheikh Muhammad al-Hafiz, da Sheikh Mahmoud Khalil Al-Hussary, da Sheikh Ahmad Nur al-Barni, da Sheikh Muhammad Zakariya al-Kandahlawiy, da Sheikh Ibrahim Nyass Kaolac, da sauran su.

 

Ɗaya daga cikin mafi kyawun hanyoyin ilmantarwa mai inganci da Sheikh Ibrahim Saleh ya gano tun da wuri shi ne, duk ɗalibin da ke son zama malami, dole ne ya zaƙulo wasu nau’ikan malamai daga cikin al’ummomin da suka gabata, kuma ya yi ƙoƙarin koyi da su.

 

Daidai da wannan dabara, ya tashi don yin koyi da tsara rayuwarsa a cikin tsarin Al-Ghazali. Al-Hafiz bin Hajaral Asqalani, dangane da Hadisi; da Abdulwahab Sha’arani, ta fuskar samar da ilimi da dama, da kuma gwargwadon ƙoƙarin sauran malamai na wannan zamani.

 

Tasirin waɗannan manya-manyan malaman musulmi a rayuwar Sheikh Ibrahim Saleh ya haskaka.

 

Ba kamar yawancin mutanen zamaninsa ba, Sheikh Ibrahim Saleh ya kiyaye rashin kwanciyar hankali a tsakanin tsarin zamani na neman ilimin addini, da kuma rungumar al’adar Musulunci da ta daɗe ta na tantancewa da ba da shaida ga malamai.

 

Ana cikin haka ne yunƙurin da ya yi na kwatanta rubuce-rubuce da sauran malamai, da kuma miƙa kansa gare su domin a yi musu bincike mai zurfi, ya kai shi manyan cibiyoyi masu daraja ta ilmin addinin Musulunci da ilmantarwa a Najeriya da ma nahiyar Afirka.

 

Misali, a shekarar 1963, Sheikh Ibrahim Saleh ya tafi ƙasar Saudiyya a karon farko da nufin yin aikin Hajji da kuma samun takardar shaida (ko ijaza) a fannin Hadisi da karatun Al-kur’ani da sauran rassa na ilimin addini.

 

Ya gana da wasu daga cikin manya-manyan malamai da ake girmama su da kuma sanin su a fagage kamar: Sheikh Umar bin Ali Al-Faruq Alfullati, Sheikh Alawi bin Abbas Al-Maliki, Sheikh Muhammadul Arabi Al-Tubbani da Sheikh Hassan bin Ibrahim Al- Sha’ir. Duk sun same shi ya isa ya mallaki takardun shaida. Haka zalika, a ƙasar Masar, Sheikh Ibrahim Saleh ya samu amincewar da ta dace a fagen Hadisi daga Sheikh Muhammadul Hafiz, da sauran fagagen da suka haɗa da karatun Al-kur’ani daga Sheikh Mahmud Khalil Al-Husari da Sheikh Amir bin Usman Al-Sayyid.

 

Sauran malamansa da suka ba da shaidar ƙwarewarsa a fannin Hadisi sun haɗa da; Sheikh Ahmad Nur Al-Barmi daga Pakistan, Sheikh Muhammad Zakariyya bin Yahya Al-Khan Dahlawi daga Indiya, da kuma shahararren malami kuma jagoran ɗarikar Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Nyass daga Senegal.

 

Ya na iya zama abin farin ciki sanin cewa, Sheikh Ibrahim Saleh ya yi shekaru ashirin ne kacal (1944-1964) a matsayin ɗalibi, kuma ya samu kusan dukkan horon da ya yi a Najeriya. Duk da haka, wannan ba ya na nufin cewa dukkan malamansa ƴan Najeriya ne ba. Amma duk da haka, ya kasance masani na gida, wadda aka samar a cikin gida ta hanyar tsarin Tsangaya.

 

Watau, horon da ya samu a cikin tsarin karatun gida ne ya ba shi damar kasancewa mashahuri a ƙasashen duniya, da kuma karrama shi a matsayin ƙwararren malami.

 

Waɗannan su ne mas’alolin da malamai suke magana a kai: nasikh wal mansukh ko asbabul nuzul. Ya na kuma iya bayar da dukkan waɗannan bayanai a kan kowace ayar Al-kur’ani, sai dai in da raunin ɗan Adam ya gaza.

 

Bayan waɗannan fagage, Sheikh Ibrahim Saleh ya bayar da muhimmanci sosai ga karatun Tauhidi da Fiƙihu. Ya kuma karanta mafi yawan muhimman littattafan da ake da su a kan tauhidi. Sannan kuma ya fahimci tushe da yanayin bambance-bambance a tsakanin mazhabobi. Fiƙihu na Mazhabar Malikiyya shi ma wani sarari ne a wurinsa.

 

Sai dai kuma, Sheikh Sharif, ya ce ya fi sha’awar ɓangaren ilimin Al-Ƙur’ani da Hadisi kuma a nan ne ya fi ƙwarewa. Sannan ya haddace Hadisan da suke cikin Bukhari da Muslim da sauran manyan litattafan hadisai.

 

Hakan kuwa ya samo asali ne sakamakon mu’amalar da yake yi da masana da mabiya sauran mazhabobi.

 

Wasu daga cikin ayyukansa su ne; Kafa Kwalejin Kimiyya da Ilimin Addinin Musulunci (Annahda), a shekara ta 1957.

 

A shekarar 1963, Sheikh Ibrahim Saleh ya yi aiki wajen gudanar da ayyukan gwamnatin yankin Arewa, wadda ya nemi shigar da makarantun Tsangaya cikin tsarin ilimin zamani, a lardin Borno.

 

A lokacin da gwamnatin jihar Borno ta kafa kwalejin koyar da shari’a da addinin musulunci ta Borno (BOCOLIS) an nada shi ne domin ya taimaka wajen tsara shirye-shiryenta na ilimi.

 

Kuma daga baya ya zama mamba na Hukumar Gudanarwa na Makarantar. Haka nan, daga 1984 zuwa 1990, ya zama Shugaban Hukumar. Amma a shekarar 1990 aka sake naɗa shi Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jiha. Ya kuma kasance a sabon ofishin nasa na kusan shekaru biyu, sannan aka mayar da shi tsohon muƙamin sa na (BOCOLIS) a matsayin Shugaban Hukumar Gudanarwa.

 

Sheikh Ibrahim Saleh, ya kuma ƙulla kyakkyawar alaƙa da gwamnatoci daban-daban tun daga 1976, a matakin tarayya.

 

Ya kasance mamba na kwamitocin da ake kafawa don ba da shawara ko jagoranci gwamnati kan wasu manufofinta da ke da alaƙa da addini.

 

Ya kuma kasance ɗaya daga cikin waɗanda gwamnatin ƙasar ke yawan tura wa zuwa ƙasashe a matsayin wakilan gwamnati ko kuma cikin wata tawaga zuwa ƙasashe kamar; Saudi Arabiya, Iran, Masar, Turkiyya, Libiya, Morko, Malaysia, Indonesia, Pakistan, Senegal, Iraq, Sudan, da sauran su.

 

Haka kuma an gayyace shi da dama domin gudanar da Tafsiri a gidan gwamnati da ke Legas, a cikin watan Ramadan, daga shugabannin da suka gabata daban-daban.

 

Ya kasance a sahun gaba wajen shirye-shiryen ƙarfafa haɗin kan Musulmi da tattaunawa tsakanin addinai domin samun zaman lafiya a Najeriya da ƙasashen waje.

 

A cikin wata hira (BBC Hausa) ya ce, ya kamata malamai su daina hauragiya da zage-zagen juna. “Kamata ya yi su haɗa kai wajen ilimantar da al’umma.”

 

Sannan ya kuma koka kan yadda ya ce ake siyasa a Najeriya ba don ci gaban al’umma ba.

 

Sheikh Ibrahim Saleh, ya na da ɗalibai da almajirai masu tarin yawa a fadin ƙasashen musulmi da na larabawa, su na kuma neman shiriya ta addini da inganta karatun boko.

 

Haka nan, mabiyansa a kodayaushe su na tare da shi ta kowane fanni da ya shafi rayuwar su. An kuma rubuta wasu daga cikin ƙasidunsa da littattafansa kai-tsaye ga wasu batutuwa na shari’a da koyarwa.

 

A cikin babban fagagensa na sha’awar ilimi da bincike, ya rubuta litattafai da ƙasidu sama da ɗari huɗu (400), da kuma takardu a wajen gabatar da taro sama da ɗari (100), waɗanda duk a cikin harshen Larabci, sun haɗa da: Ilimomin Al-kur’ani, Hadisai, Tarihi, Falsafa, Fiƙihun Musulunci, Ilimin Taurari, Adabin Larabci, Ilimin Harsuna, Kimiyyar Sufanci, Siyasar Musulunci, Dokokin Musulunci da Matsayar Gado, Zaman Lafiya Tsakanin Ƙasashe, Ainihin mutuntaka da ƴancin kai, da kuma sauran batutuwa daban-daban.

 

Baya ga ɗimbin ayyukan koyarwa da bincike, Sheikh Ibrahim Saleh ya kuma jagoranci ko shiga cikin ayyukan ƙungiyoyin Musulunci na ƙasa da na ƙasa da ƙasa tsawon shekaru, wadda sun haɗa da;

 

* Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci (SCIA) da Jama’at Nasril Islam (JNI).

 

* Shugaban Majalisar Musulmi a Najeriya (AMIN).

 

* Shugaba kuma wadda ya kafa ƙungiyar Islamic Renaissance Organization International (IROI).

 

Mataimakin Babban Sakatare Janar na Jagorancin Jama’ar Musulmi na Duniya (GIWPL), har zuwa 2010.

 

* Mamba a Majalisar Harkokin Addini ta Najeriya (NIREC).

 

* Mamba a Vision 2010.

 

* Wadda ya kafa kuma Memba na Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta Duniya (IFMS), Makka.

 

* Mamba a Majalisar Zartarwa ta Ƙungiyar Malaman Musulmi ta Duniya (IUMS), Ireland (tare da hedikwata a Doha har 2010).

 

* Shugaban Kwamitin Ba da Shawarar Kuɗi na Ƙwararru (FRACE), na Babban Bankin Najeriya (CBN). Shi ne Shugaban Sashen Shari’a na Kasuwancin Musulunci, (CBN) tun 2012.

 

* Ɗaya daga cikin waɗanda suka Majalisar Dattawan Musulmi (CME) Abu Dhabi United Arab Emirates.

 

* Mamba A Cikin Kwamitin Amintattu na Hukumar Ba da Agaji ta Duniya.

 

* Mamba na Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Yaɗa Addinin Musulunci (Sudan).

 

* Wakilin Kwamitin Amintattu Musxaf Afriqiya (sudan).

 

* Mamba Kwamitin Amintattu na Majalisar Karatun Al-kur’ani, Jihar Borno.

 

* Mamba Kwamitin Amintattu na Masallacin Ƙasa, Abuja.

 

* Ɗaya daga cikin wadda suka damar da Ƙungiyar Malaman Musulunci a Afirka (Morocco).

 

Sakamakon haka, tare da jinjinawa da irin gudunmowar da ya bayar ga addinin Musulunci, da kuma ci gaba da ƙoƙarin da yake yi na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin mutane mabambantan ra’ayi, Sheikh Ibrahim Saleh ya samu lambobin yabo ta ƙasa da ƙasa. Waɗannan sun haɗa da:

 

1. Takardar shaidar karramawa daga Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa reshen jihar Borno, 1985.

 

2. Kyautar lambar yabo ta Masarawa ta farko a fannin fasaha da kimiyya (Wisam Al-Jamhuriya), wadda shugaban Masar, Muhammad Hosni Mubarak, Jamhuriyar Larabawa ta Masar, ya bayar, 1993.

 

3. Shaidar karramawa daga hannun Ɗalibai na ɓangaren Lauyoyi, na Jami’ar Midogray, 1995.

 

4. Shaidar daga Karramawa daga Ɗalibai na ɓangaren Shari’ar Addinin Musulunci, 1995.

 

5. Takardun Shaidar Yabo daga Sashen Agajin Gaggawa na Jama’atul Nasirul Islam Group, 1996.

 

6. Takardar shaidar karramawa da lambar yabo ta Da’awah ta Musulunci, wadda cibiyar Abi Alnnour Islamic Foundation da Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Syria, 1997 suka gabatar.

 

7. Kyautar Daraja ta Farko ta Majagaba a cikin Hidimar Al’umma (Wisam Elriyada), wadda Jagoran juyin-juya halin Libiya Kanar Mu’ammar Gaddafi, Libya, 1998 ya bayar.

 

8. Lambar Yabo ta (Dir’a-Daawah), wadda Ƙungiyar Kira Zuwa Ga Addinin Musulunci ta Duniya, Libya, 1998.

 

9. Lambar Yabo ta “Al-Imam Abu Ala’za’m” (Imam Gold Medal), Alƙahira, 1998.

 

10. Kyautar Daraja ta Farko a kan Rubutu (Afro-Asian Writer of the Year 2004), wadda Ƙungiyar Afro-Asiya ta Masar ta gabatar, Alƙahira, 2004.

 

11. Kwamandan oda na Niger (CON), wadda shugaban ƙasa (Umaru Musa Ƴar’adua) kuma babban kwamandan rundunar sojojin tarayyar Najeriya, Abuja, 2008, ya gabatar masa.

 

12. Digiri na uku na Kimiyya (HNORIS COUSA) da aka ba shi, a wajen taron karo na Uku na Jami’ar Turkish Nile ta Najeriya da ke Abuja, ranar Asabar, 13 ga watan Yuni, 2015.

 

Bugu da ƙari, an sanyawa wane Masallaci sunansa a Jamhuriyar Nijar, (Sheikh Sharif Ibrahim Ibn Saleh Mosque, Niger).

 

MADOGARA:

 

1.”Highest ranking Islamic figure, Grand Imam of al-Azhar, visits Nigeria” 19 May 2016. Retrieved 2019-09-16.

 

2. “The muslim 500”. Retrieved 2014-09-16.

 

3. “King Mohammed VI Defense of Islam Sets ‘Modern’ Model: African Ulema.” Morocco World News. 2017-12-09. Retrieved 2019-09-18.

 

4. “Shaykh Ibrahim Ibn Saleh”. 23 October 2020.

 

5. Idris Ahmed (14 January 2013). “Nigeria: CBN Inaugurates Financial Regulation Advisory Council of Experts”. allAfrica. Daily Trust. Retrieved 8 February 2023. (subscription required)

 

6. “Annahada first aid group of Nigeria Maiduguri”. www.facebook.com. Retrieved 2019-09-18.[user-generated source]

 

7. “General secretariat for fatwa authorities worldwide”. Retrieved 2019-09-16.[permanent dead link]

 

8. “Buhari, Sultan, Saleh listed among world’s top 50 Muslim leaders”. 3 October 2015.

 

9. Muhammed, Isiyaku (2019-09-27). “Jibi za a kaddamar da Gidauniyar Cibiyar Sheikh Sharif Saleh”. Aminiya (in Hausa). Archived from the original on 2019-09-30. Retrieved 2019-09-30.

 

10. “Ibrahim Salih.”

 

11. University, Nile (2015-06-13). “#Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Alhussaini giving his #acceptance #speechpic.twitter.com/RKIUTalDLf”. @nileuni. Retrieved 2019-09-18.

 

RUBUTAWA

Salahuddeen Muhammad

 

Yadawa

DAUDA GWANI AHMED. HADEJIA

Share

Back to top button