CIKIN HOTUNA: Yadda Aka Gudanar Da Gagarumin Zikirin Juma’a Da Yiwa Ƙasa Addu’an Zaman Lafiya A Garin Kano.

Yadda Aka Gudanar Da Gagarumin Zikirin Juma’a A Fadar Sarkin Kano.

 

Dubban al’umma Musulmi ne suka gudanar da gagarumin taron Zikirin Juma’a na shekaran Musulunci wanda ya gudana a fadar mai martaba sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero,

 

An samu halartan manyan jami’an gwamnati, shehunai, mukaddamai, malamai da sauran al’umma daga sassan daban daban na fadin najeriya.

 

Taron Zikirin ya gudana gudana karkashin jagoranci Maulana Sheikh Dahiru Bauchi RA wanda ya samu wakilcin Sayyadi Alh Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi (Khadimul Faidah) tare da mai martaba sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero.

 

Allah ya karbi addu’o’in mu ya bamu zaman lafiya a najeriya baki daya. Amiin

 

Daga: Babangida A Maina

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button