Da ace cancantane zai sa mu zama alu’mmar ANNABI S.A.W to dukkanmu sai mun zamo Annabawa ma’asumai kafin a bamu Annabi S.A.W.

Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA yana cewa:

 

Da ace cancantane zai sa mu zama alu’mmar ANNABI Muhammadu S.A.W to dukkanmu sai mun zamo Annabawa ma’asumai kafin a bamu ANNABI MUHAMMADU S.A.W. in anyi haka to shine an turo wanda ya cancanta wa mutanen da suka cancanta,

 

Maulana yaci gaba da cewa ba da kai Na fadaba! A’a Allah ne da ksnsa yake fada a cikin Alqur’ani mai girma cikin Suratul “Ali Imran” :

.

“WA IZ AKHAZALLAHU MISAQAN NABI’INA LAMMA ATAINAKUM MIN KATABIN WAHIKMATIN SUMMA JA’AKUM RASULUN MUSADDIQAN LIMA MA’AKUM LATUMINUNNA BIHI WALI TANSURUNNA QALA AKHRARTUM WA AKHAZTUM ALA ZALIKUMU ISRI QALU AKHRARNA QALA FASH HADU WA’ANA MA’AKUM MINA SHAHIDIN”.

.

Ma’ana Allah yake ce ma ANNABI S.A.W ka tuna lokacin da muka dauki Alkawari mai karfi da Annabawa bayan mun basu sako suna cikin isarwa sai wani babban manzo yazo musu wato “Annabi Muhammadu” kenan

.

Allah ya tambayi Annabawan nan shin

zakuyi Imani dashi sannan zaku taimake shi wato kamar muhajiruna da lansaru kenan, suka ce Allah mun yarda .

.

Sai Allah yace to Ku shaida nima Na shaida

.

Maulana Shehu Dahiru yace misali kamar dai shugaban kasa ne ya zabi ministoci kafin a rantsar dasu sai a karanta musu dokokin office da sharudda idan sun amince a tabbatar musu to haka Allah S.W.T yayi da Annabawa kafin kowani Annabi ya zama cikakken Annabi.

 

Sai da yayi alkawari a gaban Allah cewa da yayi zamani da ANNABI S.A.W da ya kwabe rawaninsa Na Annabta yabi Annabi Muhammadu SAW kamar yanda muhajiruna da lansaru suka bishi wannan shine sharadin nadin dukkan Annabawa

 

Sai da suka amice da haka suka zama Annabawa to inka dubi karatun shi ANNABI S.A.W.

 

Wato ANNABI ne da aka turu ma Annabawa don Allah yace “Summa ja’akum Rasulun’ .

 

A nan da Annabawa akeyi kuma Allah yasaka ce musu “Latuminunna bih”.

.

Za kuyi Imani da shi namma da Annabawa akeyi ba da muba.

.

Annabawa da suke kira ayi Imani sai gashi ana kiransu suyi Imani da wani babban MANZO S.A.W.

.

To Allah S.W.T cikin ikon sa wannan ANNABIN ALLAH yake kiran Annabawa suyi Imani dashi

 

Sai gashi kwatsam Allah ya bamu shi a Arha ya kamata mu gode ko kuma A’a? .

 

Lalle idan bamu gode ma Allah ba to munyi babban butulcin da ba’a taba irin sa ba dole mugode shiyasa wasu jama’a har yanzu basu manta ba duk randa watan haihuwar wannan babban ANNABI ya zago sai sun nuna murna don godiya ma Allah.

 

Maulana Shehu Dahiru Allah ya saka da Alkhairi Allah ya kara Maka lafiya da Nisan Kwana Bijahi S.A.W. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button