DARUSA AIKIN HAJJ: Yanda Zaka Gudanar Da Aikin Hajji Cikin Sauki.

ABUBUWAN DA AKE SO MAI SHIGA MAKKA YA YI…
An so ga duk wanda zai shiga garin Makka ya yi wanka da niyyar shiga garin. Bayan wankan da mai Hajji ko Umura ya yi na ɗaura Harami, an so idan zai shiga Makka ya yi wani wankan, amma ba dole ba ne.
An so ga wanda zai shiga Makka ya kwana a wurin da ake ce ma Ziɗuwan saboda Annabi (SAW) da ya zo, ya kwana a nan. Ana so mutum idan zai shiga garin, ya shiga ta saman Makka (da yake garin kamar tudu da kwari ne).
Ana so idan mutum ya shiga Makka bayan ya ajiye kayansa a amintaccen masauki, ya yi gaggawan zuwa Harami. Ya shigo ta Babus Salam (a da; nan ne Babub Bani Shaiba take, sannan da ka shigo ga ƙofar Ka’aba nan). Idan za a shiga, a tabbatar da yin ƙanƙan da kai ga Allah kuma a karanta wannan addu’ar, “A’uzu billahil aziym, wa bi wajhihil kariym, wa sulɗanihil ƙadiym minas shaiɗanir rajiym bismillahir rahmanir rahim, bismillah, allahumma salli ala Muhammadin wa alihi wa sallim, allahumma agfirliy zunubi, waftahali abwaba rahmatika”.
Ma’anar addu’ar ita ce, “Allah ina neman tsari da kai, ya Ubangiji maigirma, da hasken fuskarka (yadda ya dace da shi) maigirma, da sarautarka dauwamammiya, daga shaiɗani abin jefewa, da sunanka Allah, Allah ka yi salati ga Annabi Muhammad (SAW) da ‘ya’yan gidansa, ka yi aminci a gare shi. Allah ka gafarta mun zunubina, Allah ka buɗe mun ƙofofin rahamarka.”
Ba a Harami ba kawai, a kowane Masallaci an so a karanta daga kan salatin Annabin nan zuwa ƙarshen addu’ar idan za a shiga.
Idan mutum bai iya wannan addu’ar ba, ya yi a’uziyya da bisimillah da salatin Annabi (SAW) da kuma addu’ar da ya iya.
Ana so da zarar mutum ya shiga idanunsa sun kalli ɗakin Ka’aba, ya ɗaga hannu ya nuna ɗakin ya ce “Allahumma zid haazhal baita tashriyfan wa ta’aziyman wa takriyman wa mahaabatan wa zid man sharrafahu wa karramahu min man hajjahu awi’itamarahu tashriyfan wa takriyman wa ta’aziyman wa birran, Allahumma antas salamu wa minkas salamu fahayyina rabbana bissalam.”
Ma’anar addu’ar ita ce “Allah ka ƙara wa wannan ɗakin ɗaukaka da girma da kwarjini, Allah duk wanda ya girmama shi, ya daraja shi a tsakanin wanda ya hajja ce shi ko ya yi umura, shi ma ka ƙara ma sa ɗaukaka da girma da buwaya da tsoronka da bin ka. Allah kai ne aminci, daga wajenka aminci yake zuwa, mun gaida Ubangijinmu tare da sallama.”
Daga nan sai mutum ya nufi Hajrul As’wad ya sumbance shi da bakinsa, idan bai samu iko ba ya shafa da hannu sai ya sumbanci hannun, idan ma wannan bai yiwu ba, to ko daga nesa yake ya nuna wurin dutsen da niyyar ya taɓa sai ya sumbance shi da hannu. Akwai alamar da aka sanya na tiles wanda aka ja layi da shi tun daga Hajral As’wad ɗin har zuwa bango har cikin gine-ginen saitin wurin, a nan mutum zai tsaya ya yi sumbar idan bai samu isa kaiwa ga dutsen ba. Daga nan sai ya fara ɗawafi.
Hajral As’wad yana da girman daraja a Musulunci, Annabi (SAW) ya ce “duk wanda ya sumbance shi zai yi ma sa shaida a ranar Tashin ƙiyama.” Sannan ya zo a Hadisi cewa dutsen hannun daman Ubangiji ne (yadda ya dace da shi).” Ire-iren waɗannan Hadisin ba a iya gane haƙiƙanin ma’anarsu sai dai a karɓe su a matsayin ibada.
Idan an shiga Ka’aba ba a yin nafilar gaisuwar Masallaci, ɗawafin da Alhaji ko mai Umura zai yi shi ne yake makwafin nafilar, amma ga wanda ba Hajji ko Umura yake yi ba, shi zai iya yin nafilar. Idan kuma mai yin Aikin Hajji ko Umura ya shigo ya ga an tada sallar farilla, sai ya bi, ba zai ce sai ya kammala ɗawafi ba. Koda mutum yana cikin ɗawafin ne aka tsaida sallar farilla, zai yanke ɗawafin ya tsaya daidai inda yake ya kabbara sallah. Ana yin sallama sai ya ci gaba da yin ɗawafin.
Kamar yadda muka yi bayani a baya, ana fara ɗawafi ne daga Hajrul As’wad bayan an sumbance shi ko an shafe shi ko ɗaga hannu. Mutum zai sanya Ka’aba a hagunsa sai ya ce “Bismillah wallahu akbar, Allahumma imanan bika wa tasdiyƙan bikitabika wa wafaa’an bi ahdika wattiba’an lisunati Nabiyyika.”
Ma’anar addu’ar ita ce “Ina farawa da sunan Allah, Allah kai ne maigirma, zan yi ɗawafin nan ne don imani da kai da gaskata littafinka da cika alƙawarinka da bin sunnar Annabinka (SAW)”.
Haka mutum zai je ya kewayo, sai ya riƙa ƙirgawa duk lokacin da ya zo kan layin nan da ya fara ɗawafin daga kansa har ya yi guda bakwai. Idan namiji ne, ana so ya yi sassarfa a kewaye na ukun farko, sauran kuma ya yi tafiya Idan kuma an cika da yawa ta yadda mutum ba zai iya yin sassarfar ba sai ya yi tafiya kawai, babu komai. Amma mata ba su yin sassarfa, duka nasu tafiya ce.
Ka’aba tana da kusurwowi guda biyu, Kusurwar Hajrul As’wad da ake farawa da ita, sai kuma wasu guda biyu da aka yi musu shinge su biyu ta yadda mutum ma ba zai iya taɓawa ba (Tarihi ya nuna cewa waɗannan kusurwowin biyu, nan ne lokacin da ƙuraishawa suke gina Ka’aba da kuɗinsu na halas ya ƙare sai suka datse ginin), su waɗannan ba a taɓa su ko an zo wucewa ta wurinsu. Amma idan mutum ya kewayo kafin ya zo Hajrul As’wad akwai Kusurwar Rukunil Yamani wanda shi ma ana shafarsa idan an samu hali, idan babu hali sai a nuna shi da hannun dama. Za a riƙa yin haka a duk kewayen ɗawafin da za a yi.
Ana so a yawaita Zikirin Allah da addu’o’in da mutum ya zaɓa ya yi, don Malamai sun ce babu wata addu’a da aka ce dole ita za a yi. Sai dai wanda Hadisi ya kawo na Hajral As’wad. Addu’o’in da ake rubutawa a littafan nan da ake karantawa na Aikin Hajji masu kyau ne amma ba wai dole sai su ba. Idan mutum yana ɗawafi sai ya yawaita faɗin Subhanallah wal-hamdulillah wa la’ilaha illallah wallahu akbar wa laahaula wa laa ƙuwwata illa billahil aliyyil aziym, kamar yadda Ibn Majah ya ruwaito.
A wurin Rukunil Yamani kuma, Abu Dawuda da Imamus Shafi’i sun ruwaito Hadisi daga Annabi (SAW) ya ce idan aka zo nan za a iya karanta “Rabbana atina fid dunya hasanatan wa fil-akhirati hasanatan wa ƙina azaban nar”. Akwai Mala’iku a wurin da za su amsa wa mutum da amin. Za a iya yin wannan addu’ar a lokacin gudanar da ɗawafin baki ɗaya.
Zuwa mako mai zuwa za mu ci gaba da wani darasin cikin yardar Allah inda za mu kawo yadda Manzon Allah (SAW) ya yi aikin Hajji. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi haƙƙa ƙadrihi wa miƙdarihil aziym.