Daya Daga Cikin Malaman Tijjaniyya Sheikh Goni Ayuba Alkarasamy Ya Assasa Makarantun Da Dama A Najeriya.

ABINDA YA KE YI, SHINE JADDADA SUFANCI A ZUKATAN YARA MASU TASOWA.

 

Dayan mu, ba zai fahimci girman aikin da wannan hazikin bawa na ALLAH yake yi ba, sai ya rayu zuwa tsawon shekaru, idanunsa sun nuna masa sakamakon aikin da jajircewarsa ta haifar.

 

Idan ka zauna ka nazarci tsarin da yake assasa makarantunsa na Darul Kur’an akai, anan zaka fahimci fadin tunaninsa, domin tsarine wanda :-

 

1- Tun daga Matakin Primary yaro zai koyi hada baki, haddace Kur’ani ya rubuta, sanin Litattafan Fikhu, da kuma haddace wasu daga littattafan Sufanci, da kuma koyon harshen larabci da turanci, da koyar da dabi’un Sufanci na ainashi.

 

2- A matakin Secondary za’a kokarin fadada abinda dalibi ya koya a Primary, sannan a tabbatar da kwarewarsa cikin abinda yafi fahimtsa cikin Art ko kuma Science, sannan bayan kammala Secondary sai a tsaya masa wajen ganin ya shiga jami’a.

 

Lallai ne, ya zamanantar tare da kyautata tsarin Makarantar Allo zuwa yadda aka sirka zamani wajen cimma manufa.

 

ALLAH YA KARAWA SHEIKH Goni Ayyub Al-Karamsami LAFIYA DA TSAWON KWANA. Amiin Summa Amiin

 

Daga: Muhammadu Usman Gashua.

Share

Back to top button