Dole A Kamo Waɗanda Suka Saki Bom Kan Masu Mauludi, Kuma A Hukunta Su. Inji Sheikh Dahiru Bauchi.

BA ZAMU LAMUNTA BA: Dole A Kamo Waɗanda Suka Saki Bom Kan Masu Mauludi, Kuma A Hukunta Su

 

………- Cewar Shaikh Dahiru Bauchi RA.

 

Babban Malamin addinin Musulunci A Najeriya Maulanmu Shaikh Dahiru Usman Bauchi yayi kira na gaggawa ga hukuma kan Kisan masu Mauludi yace gwamnati ta daina wasa ana kashe rayukan mutane yace lallai wannan karon baza su bari ba, dole ne gwamnati ta fito ta kama duk wani mai hannu a kisan ta gurfanar da shi a yanke masa babba hukunci daidai da abinda ya aikata.

 

Shehin Malamin cikin wani faifan bidiyo da babban dansa Alhaji Ibrahim ya fitar ya Kara da cewa haka shekarun baya ma jama’arsu sun fito Zikirin Juma’a aka taresu aka yanka su, gashi yanzu ma an jefawa wasu Bom Dan haka baza su bari ba-Inji Shehin Malamin

 

Daga karshe Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya mika ta’aziyarsa zuwa ga iyalai wayenda abun ya shafa, tare da kira ga al’umma da su kwantar da hankalin su Lallai baza’a bari ba za’a dauki kwakkwaran mataki.

 

Daga: Sufi Media Connect.

Share

Back to top button