Dole A Yaƙi Bidi’a, Dole A Yaƙi Abubuwa Na Ɓata Da Aka Shigar Dasu Cikin Addini. Cewar Farfesa Ibrahim Maqari Hafizalullah.

Maulana Prof. Ibrahim Maqari Yana Cewa;

 

“Babu Shakka Dole A Yaƙi Bidi’a, Dole A Yaƙi Abubuwa Na Ɓata Da Aka Shigar Dasu Cikin Addini, Amma Ba Jahilai Ne Ke Yaƙan Ɓata Ba, In Ja@hili Yazo Yace Zai Ya*ƙi Ɓata Zai Haɗa Shiriya Da Ɓa@ta Duk Ya Ƙirasu Ɓata Malamai Su Suke Yaƙan Ɓata@”

 

Maulana Prof. Ibrahim Maqari Ya Ƙara Da Cewa;

 

“Babu Shakka Akwai Ɓata Cikin Al’ummar Musulmai, Babu Shakkah Akwai Bidi’o’i Cikin Al’ummah, Kuma Babu Shakka Kaucewa A Hanya Cikin Al’umma, Amma Ba Ja@hili Ne Zai Gyara Wannan Ba”

 

Ya Ƙara Bada Misali Inda Yake Cewa;

 

“Idan Jahi@li Wanda Bai San Ya Ake Operation Ba Yazo Ya Samu Mara Lafiya Yaga Ciwo A Jikin Sa Yace Zai Masa Operation Kisa Zaiyi.

 

To Mai Yasa Sai Addini Ne Ake Ma Wannan Riƙon Sakainar Kashin? Ko Wane Jahili Ya Buɗe Baki Yace Zai Gyara ? Ba Munga Ciwon Ba? Me Yasa Bazamu Cewa Ja@hili Ya Farke Cikin Ya Gyara Ba?”

 

Sai Imam Ibrahim Ahmad Maqari Ya Bada Amsa Da Kansa Yace;

 

“Saboda Ba Masanin Wannan Layin Bane, Shi Kaɗaine Ba Don Baisan Ciwon Bane, Ba Don Bai Ganin Ciwon Bane A’a, Don Ba Layinsa Bane Magance Wannan Ciwon, Ciwon Yana Ɗauke Da Ilimomi Da Dama Da Sai Anje Anyi Karatun Su, Amma Zai Iya Ganin Ciwon”

 

Maulana Professor Ya Cika Da Mana Nasiha Inda Yace “Wa@llahi Muyi Wa Kanmu Adalci” Muna Ƙara Miƙa Godiya Da Prof. Tare da Addu’a Game Da Fatan Allah Ya Saka Masa Da Alkhairi. Amiiiin

 

Daga: Izzuddin Sadauki Shehu Manzo

Share

Back to top button