Don haka masu cewa mubar Darika bata da kyau to suzo su bamu abunda yafi Darikar mana sai mukama abinda suke son. Inji Sheikh Dahiru Bauchi OFR RA.

Maulanmu Sheikh RTA Yana cewa;

 

A lokacin da Allah (S.W.T) ya baiwa Annabi Musa (A.S) nasara akan fir’auna, bayan ya ketare kogi tare da tawagarsa da sukayi imani dashi daga cikin “banu isra’ila”.

 

Saboda tsananin bautar da suka saba yiwa fir’auna su “banu isra’ila” abaya Sai suka cewa Annabi Musa (A.S); kabamu wani aiki mana muyi maka kamar yanda muka sabayiwa fir’auna mana ada??

 

Sai Annabi Musa (A.S) yace musu ai yanzu bautar Allah zakuyi, Amma ba wani mahaluki ba.

 

Sai ya koya musu yadda ake bautar Allah. To kunga kenan ya basu wani abunda yafi wanda suke kai a baya.

 

To haka akeyi idan har ka hana mutune abunda sukeyi kace babu kyau, to sai ka basu wani aikin mai kyau wanda yafi wancan din.

 

Don haka masu cewa mubar Dariqa.

 

bata da kyau toh suzo su bamu abunda yafi Dariqar mana sai mukama abinda sukeson??

 

Mu dai ga Darikar (abinda muke a cikin ta) kamar haka;

 

1. Istighfari

2. Salatin Annabi (S.A.W)

3. Lailaha Illallahu

 

Idan aka bamu abinda yafisu sai mu barsu mubi wanda ya fisu din. Idan kuma ya kasance babu abinda yafisu kuma ace basuda kyau, to ya zamo ana gaba da zikirin Allah ne kenan a fili ba wani abu ba.

 

Saboda haka a kiyaye da masu satar Imani su raba mutum da Allah.

 

Na’am Alhamdulillah, Mungode Shehu.

 

Allah yakara Lafiya Da Tsawon Rai Albarkar Manzon Allah SAW A’min A’min

Share

Back to top button