Duk Cikin Idin Sallar Babu Kamar Idin Samun Manzon Allah (SAW) Inji Sheikh Dahiru Bauchi RA

Duk Cikin Idin Sallar Babu Kamar Idin Samun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

 

Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi RTA yace; Shehu Ibrahim Kaulaha RTA yana cewa:

 

Duk wani Murna/idi yana zuwa ne bayan wani alkairi da aka samu Azumin watan Ramadan da muke murna ne da samun Alkur’ani, Idin Sallahr Azumi murna ne da kammala azumin lafiya, Idin Babbar Sallah (Layya) murnane na (Yan’uwan mu sun hau hajji sun sauka lafiya), Sallar Juma’a Idin sati kenan Murna ne na Allah ya bamu daman yin Sallar harna tsawon sati.

 

Shehu Ibrahim RTA: yace ni kuma agu na babu wani Alkhairin da yakai Samun Annabi Muhammadu SAW a duniya, saboda haka Maulidin/Murna da samunsa yafi kowanne idi.

 

Shehu yakara da cewa: Haka kuma Shehu Ibrahim RTA yake girmama Maulidin Annabi SAW ya daukeshi babu abinda ya kaishi a cikin Iduka, harma duniya tazo tai ta koyi da irin shirin Maulidin sa da ya keyi. Ko anan Nigeria da ba’asan Maulidi ba ana kiransa, A Kano Takutaha, Wani wuri Babbar Sallah, wani wuri kuma Sallahn Kaji da sauran su, to idan Muqaddamai sun je Kaulaha sun ga yadda Shehu Ibrahim keyin Maulidi in sun dawo Nigeria sai suke koyi dashi, haka nan in kowa ya gani sai yayi tambaya wai shin wannan kam meye ne ??

 

Ace musu ai Maulidi kenan murnane da haihuwar Annabi SAW. Saisuce ah muma zamuyi, muma zamuyi inde abu na Son Annabi ne SAW baza abarmuba.

 

Haka nan yanzu in watan ta kama to babu yaro ba babba kowa yana nuna farin cikin sa da zuwan Annabi Muhammadu SAW duk albarkar samun Shehu Ibrahim RTA, Masha’ Allah

 

Allah ya sakawa Shehu Ibrahim Niasse RTA da Alhairi, Allah karawa Shehu lafiya Albarkar Manzon Allah SAW, Allah Kara mana soyayya A’min A’min

Share

Back to top button