DUK LOKACIN DA KA SHIGA CIKIN TSANANIN WAHALA DA KUMA DAMUWA KADA KA MANTA.

DUK LOKACIN DA KA SHIGA CIKIN TSANANIN WAHALA DA KUMA DAMUWA, KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA BAKWAI:

 

1. Ka tuna cewa Jarrabawa ce daga Ubangininka, wanda yafi kowa Sonka da Kaunarka.

 

2. Ka tuna cewa Ubangijinka yayi maka haka ne don ya Kankare maka Zunubanka, ko kuma ya daukaka maka darajarka.

 

3. Ka tuna cewa an jarrabi Annabawa da Manzanni da Salihan bayin Allah wadanda suka zo kafin ka.

 

4. Ka tuna cewa Tun kana cikin mahaifiyarka kafin ta haifeka an riga an rubuta maka duk abinda zaka samu aduniya, da kuma dukkan abinda zai sameka. Mai dadi ko Kishiyarsa.

 

5. Ka tuna cewar rungumar Qaddara kowacce iri, yana daga cikin Ginshikan Imaninka. Gwargwadon yadda kake rungumar Qaddara, gwargwadon haka imaninka yake.

 

6. Ka tuna cewar kowanne tsanani yana tare da sauki guda biyu. (Ga lada, ga kuma yayewar tsananin).

 

7. Ka tuna cewar Allah shine ARHAMUR RAHIMEEN (MAFI TAUSAYIN MASU TAUSAYI) kuma yafi komai kusa dakai, Kuma yafi kowa tausayinka. Kuma zai amsa dukkan rokonka.

 

Ya Allah ka yaye mana dukkan Tsanani don hasken Alqur’anin ka, don Rahamar nan taka wacce ta yalwaci dukkan halittunka Ya Amiiiin Yaa Allah.

Share

Back to top button