DUK MUSULMAN NAJERIYA SUN GANE SU WAYE MAKIYA MANZON ALLAH SAW.

DUK MUSULMAN NAJERIYA SUN GANE SU WAYE MAKIYA MANZON ALLAH SAW.

 

……Cewar Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi RTA.

 

Shugaban Gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi (Khadimul Faidha) Ya Bayyana Yanda Wasu Gaggan malaman Izala Suka Goyi Bayan Dan Uwansu Akan Kalman Batanci da Yayi Ma Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu ﷺ.

 

Sheik Ibrahim Ya Kara da Cewa Bama Goyon Baya Wannan Al’amari Na Batanci ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu ﷺ,

 

Ya Kara da Cewa ae Ba’a Raba Allah da Manzon Allah ﷺ, Raba Allah da Manzon Allah ﷺ Babban Laifi ne.

 

Sannan Yayi Kira da Jan Kunne Wa Yan Uwa Masoya Manzon Allah ﷺ, da Cewa Kowa Yasan Inda Zai Na Sallar Ibada Don Allah Ba’a Raba shi da Manzon Sa ﷺ, Duk Inda Kaji Ance Allah to Zakiji Ance Manzon Allah ﷺ,

 

Daga karshe Ya Yaba Ma Dukkanin Yan’uwa Musulmai Masoya Manzon Allah ﷺ, da Sukayi Tsayin Daka Don Kare Martaban Manzon Allah ﷺ, Yayi Addu’a Allah Ya Karfafi Musulunci da Al’ummar Musulmai Masoya Manzon Allah ﷺ,

 

Kuma Ya Kara Kira ae ta Addu’a Allah Ya Kara Tona Musu Asiri a Duk Inda Suke, Mu kuma Allah Ya Karemu Daga Sharrin Makiya Manzon Allah ﷺ.

 

Daga: Khadimul Faida Media Team Nigeria.

Share

Back to top button