Duk Musulmi Da Yaje Aikin Hajji To, Yayi Mauludin Manzon Allah SAW. Inji Sheikh Dahiru Bauchi RA
Duk Musulmin Daya Je Aikin Hajji To Yayi Maulidi – Inji Sheikh Dahiru Bauchi
Mauludi Umarnin Allah ( S.W.T.) ne- Sheikh Dahiru Bauchi
Sheikh Dahiru Usman Bauchi yace, “Idan ka ji Mutum Yana Sukar Maulidi To Ka Ce Masa; ai Maulidi Iri Biyu Ne.
A cikin zantukan Babban Malamin, ya Cigaba da cewa; akwai Mulidi Na Zamani Wato Watan Rabi’ul Auwal, a Watan Bature Kuma a afrilu Wannan Shi Ne Maulidin zamani, bisani Akwai Kuma Malidi na Makan i(Wuri) Wato Makkah da Madina.
Shehin Ya Ci Gaba Da Cewa; Idan Mutum Ya Samu Kudin Zuwa Hajji Zai Tafi Dolensa, Shin Anan Waye Ya ‘Kra Shi?? Aka Ce; Allah (S.W.T),
Don Haka Duk Wanda Ya Tafi Makkah da Madina to ya tafi Mauludin Manzon Allah (S.A.W) Ne Na Makani, inji Shi babban Malamin.
Har walayau, acikin bayanan babban Malamin, yaka da baki inda yake cewa; Zai je ya ga Inda Aka Haifi Annahi (S.A.W), Ya Ga Masallacinsa, Ya Ga Gidansa ya ga Ababen Da Aannbi (S.A.W) Yayi Rayuwa Da Su, Koba komai ya tuna da Annabi Kuma hakan Shima maulidi ne.
A karshe Jagoran Mabiya darikar Tijjaniyya, ya karkare da fashin baki Kan Haka, don Haka Kenan Dole Ne Musulmi Yayi Maulidi ko na Makani Wato Zuwa Makka da Madina, Ko Na Zamani ‘Din Wato Watan Rabi’ul Auwal.