Duk Wanda Aka Fada Masa Wani Abu Na Ilmi Sai Ya Tirje Ya Ce Lalle Sai An Kawo Masa Hujja A Lilttafi To Bai San Addini Ba.

MAULANA SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI R.A. Yana Cewa:

 

“Duk Wanda Aka Fada Masa Wani Abu Na Ilmi Sai Ya Tirje Ya Ce Lalle Sai An Kawo Masa Hujja A Lilttafi To Bai San Addini Ba, Domin Kuwa Akwai Ilmomi Wanda Basa Takarda Kuma Tun Kafin Takarda Akwai Dan Adam, Kuma Idan Aka Ce Komai A Kawo Hujja A Littafi Sai A Tambaya;

 

‘Kissar Annabi MUSA A.S. Da Sayyidina KHIDIR R.A. Lokacin Da Khidir ‘Din Ya Kama Yaro Ya Wujijjigashi Ya Buga Shi Da Garu/Bango Ya Mutu, Da Annabi MUSA A.S. Ya Tambaye Shi Menene Yasa Ya Kashe Rai Mai Yayi Maka???

 

Sai Khidir Ya Cewa Annabi MUSA Shi Wannan Yaro Da Na Kashe Shi Idan Ya Girma Zai Zama Kafiri Kuma Zai Riddantar Da Iyayensa,

 

To Ace Lokacin da Annabi MUSA A.S. Ya

Tambaye Shi A Ina Ya Gani Cewa In Yaron Nan Ya Girma Zai Zama Kafiri, Babu Amsar,

 

Don Daga ‘Karshe Khidir ‘Din Ya Fada Wa Annabi MUSA A.S. Cewa Wannan Ilmin Daga ALLAH Ne,

 

To Ya Kamata Lalle A Yarda Cewa Ba Kowanne Ilmi Bane Yake A Takarda Akwai Tilin Ilmin Da Yake ‘Kunshe A KIRAZAN BAYIN ALLAH (Salihai), Kai Shi Ne Ma Ilmi Mafi Fadi, Don Haka Nema ALLAH Yake Cewa;

 

“Wattaqullaha Wayu’allimu Kumullah”.

 

ALLAH YA QARAWA SHEHU LAFIYA DA JURIYA, YA QARA KARE MANA SHI DAGA SHARRIN MASU SHARRI AMEEEEN.

Back to top button