Duk Wanda Ya Kushe Mauludi Bagidaje Ne Ba Malami Bale. Inji Sheikh Prof, Umar Sani Fagge.

Shahararren malamin Addinin Musulunci kuma babban sufi mabiyin darikun sufaye Sheikh Prof, Umar Sani Fagge yana cewa;

 

…Duk Wanda Kushe Mauludi Bagidaje Ne Ba Malami.

 

Sheikh Umar Sani Fagge ya kara da bayyana cewa: ASALIN MAULUDI A QUR’ANI DA HADITH

 

Shi Mauludi a wurin Masoya Manzon Allah SAW yana nufin Murna da farin ciki da samuwar Manzon Allah SAW a matsayin shi na Rahama ga duk halittun Allah ta hanyoyi da dama kamar yin taro a bada tarihin Manzon Allah SAW, ajiyar da masoyi dadi dajin Qasidun Manzon Allah SAW, aciyar da mutane dan Annabi SAW kuma a sada zumunci da yanuwa duk don Murna da Farinciki da Samuwar Rahamar Allah Annabi Muhammadu SAW.

 

Allah (SWT) yayi mana Umarni dayin Farin ciki da Murna da Manzon Allah SAW kamar yadda Alqur’ani ya gaya mana a Suratul Yunus aya ta 58.

 

قُل بِفَضلِ اللَّهِ وَبِرَحمَتِهِ فَبِذٰلِكَ فَليَفرَحوا هُوَ خَيرٌ مِمّا يَجمَعونَ

 

Ka ce: “Da falalar Allah da rahamarSa, saboda wannan suyi farin ciki .” Shĩ ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa.

 

Allah yafaɗa mana yin Farinciki da samun Falalar Allah da Rahamar sa. Yafi dukkan abunda muke tarawa. Kuma Rahamar Allah a wannan ayar shine Annabi Muhammadu SAW kamar yadda Alqur’ani da hadisai suka nuna mana.

 

Imam Assayudi ya kawo a Tafseerinsa yace :

 

واخرج ابو الشيخ عن ابن عمر رضي الله عنه في الأية قال :

Abush Sheikh ya fitar daga Sahabin Manzon Allah SAW Abdullahi bn Abbas yace akan wannan ayar :

 

فضل الله العلم ، ورحمته محمد صلى الله عليه وسلم. قال تعلى ؛

 

Falalar Allah shine Ilimi,

Rahamar Allah shine Manzon Allah SAW.

Domin Allah madaukakin Sarki yana cewa :

 

وما ارسلناك الا رحمة للعالمين

Bamu aikoka ba Ya RasulalLaH face Rahama ga talikai.

 

Sannan Hadisai sun tabbatar mana cewa Manzon Allah SAaw shine Rahamar Allah.

 

1.Hakim ya ruwaici hadisi a Mistadrak hadisi na 100

 

عن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال : يا ايها الناس ، انما انا رحمة مهداة.

 

Manzon Allah SAW yace : yaku mutane lallai ni Rahama ce kyauta da Allah ya baku. .

 

Masha Allah; Allah ya kara mana kaunar Manzonsa (saw) Yabarmu soyayyan Annabi ﷺ. Amiiin Yaa ALLAH.

Share

Back to top button