Dukkan Wanda Yake Yin LALATA/ZINA Jahili Ne, Domin a Lokacin An ‘Dauke Masa Ilimi…

MAULANMU SHEIKH TAHIRU USMAN BAUCHI(R.A) Yana Cewa;

 

“…Dukkan Wanda Yake Yin LALATA/ZINA Jahili Ne, Domin a Lokacin(Da Yake Cikin Aikata Fasadin) An ‘Dauke/Kwashe Masa Ilimin Nan Na Sanin Abin Da Zai Aikata Haramun Ne,

 

Kuma Sai An Cire Masa IMANI a Lokacin Da Zai Aikata(Wannan Fasadin).

 

MISALI…..

 

Da Za’a ‘Kera MACE(Ta ‘Karfe) ‘Dauke Da Dukkan Siffofin Da Mata Ke Da Shi Sai a Sanyata Cikin Wuta(a Ziga Wutar), Sai Ƙarfen Nan(Mai Siffar Mace) Yayi Jajur,

 

Sai Ace Ma MAZINACIN Ya Rungumeta a Tsaye, Ba Sai Sun Kwanta Ba Ma, Shin Zai Aikata Hakan Kuwa???

 

To Ya Kamata MAZINACI/MAZINACIYA Su Fahimci Cewa;

 

WUTAR JAHANNAMA(Mai Ruruwa) Ce Suke Kwanciya Da Ita. Don Haka a Tuba a Koma Ga ALLAH(S.W.T)”.

 

ALLAH Ya ‘Kara Kiyaye Mu(Da Zuri’armu Baki ‘Daya) Daga Afkawa Fasadin Zina.

 

FATANMU A KULLUM SHI NE; ALLAH YA ƘARAWA MAULANMU SHEIKH LAFIYA(Ta Gangar Jiki) DA NISAN KWANA, YA BA MU ALBARKARSU AMEEEN

Share

Back to top button