FAHIMTATA GA WANNAN ZINARIYAR ZANCE NA MAULANA Prof. Ibrahim Maqari (H).
FAHIMTATA GA WANNAN ZINARIYAR ZANCE NA MAULANA Prof. Ibrahim Maqari (H).
Daga @Muhammad Usman Gashua
Ayayin da ANNABI (S.A.W) yayi hijira daga Makkah zuwa Madina an kira zama da kabilun Yahudawa dake Madina irinsu : Banu Najjar, Banu All-Haris, Banu Sa’idah, Banu Jusham, Banu al-Aws, Banu Sa’labah, Banu Jafnah, Banu al-Shutaybah da sauransu.
Ayayin wannan zama, an zartas da wasu yarjejeniyoyi wadanda suka karfafi alaka tsabtacecciya tsakanin kishin Addini, Kishin Kasa, Kishin yanki, kishin yare, ta hanyar fuskantar abinda zai kawo ci gaba ga dukkanin al’ummar Madina, tare da kare musu kima, rai, dukiya da mutunci daga makiyan waje.
Aciki har aka zartas da cewa “Idan aka kawo hari Madina, ko wasu sashe na al’ummarta (Musulmi ko Yahudawa) to haduwa za’ayi baki daya wajen baiwa juna kariya ba tare da duba kowanne irin wariya ba.
Amma mu a yau a Nigeria, Malaman Addini da kuma jagororin al’umma, sun kasance suna masu fifita bangarancin Addini, Yanki, da kuma yare a matsayin itace maslaha, mai-makon haduwa bisa tsari na gamayya, tare da fifita dafawa wanda ya chanchanta wajen gina kasa yadda kowa zai amfana ta hanyar barin bambance-bambance.
Ko Ma’aikatu ka tafi, anfi damuwa da daukar wanda aka hada yare, addini, da yanki dashi ko da bai chanchanta da gurbin da za’a sanya shi ba, daga barin wanda ya chanchanta da ake da bambance-bambance da shi.
Idan muka lura da kasashen da sukaci gaba, irinsu Amurka da Birtaniya, sun kai ga matakin da suke ne, ko a yayin da suka dauki maslahar kasarsu sama da maslahar kowanne irin bambanci, wanda hakan har ya bayar da dama Obama da yake tsatson Africa ya zamo Shugaban Kasar Amurka, Saqiq Khan dake Musulmi tsatson Pakistan ya zamo Magajin garin Birnin London.
Atakaice dai ayau Kishin kasa shine aji na karshe wajen mutanenmu a kowanne mataki wanda hakan shine yake haifar mana da rigingimun kabilanci, koma baya ta fuskar tattalin arzki, da sauransu.
ALLAH YA KARA HASKAKA KIRJIN WANNAN JAGORA, DA YA KASANCE MA’ABOCIN