Farfesa Ibrahim Maqari RA, Ya Fayyace Gaskiya Akan Al’amuran Rayuwa.

YADDA BATUN YAKE (A FAHIMTATA).

 

Dukkanin ANNABAWAN ALLAH sun kasance da wata sana’a da suka dogara da ita, wasu noma, wasu kira, wasu kiwo, wasu su wasu fatauci da sauransu baya ga aikin da aka aiko su da shi.

 

Hakanan dukkanin halifofinsu nagartattu (Daga Malamai) basu kasance cima zaune ba, kowanne guda cikinsu ya tsaya da kafafunsa wajen yin kasuwanci domin samun abin dogaro, misali Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass (R.T.A) da shuhurarsa ta fannin noma da kiwo a matsayin sana’arsa abar riko.

 

Idan kayi duba zuwa zaben da ya gabata kadai zaka fahimci lallai a yau dayawa daga masu wadannan siffofi da aka ambata (Malamai) sun kasance ababen tausayi, domin kowanne guda cikinsu kokari yake yaga ya tallata wani dan Siyasa da siffofin da shi kansa yasan bai da yakini akan ingancinsu, a takaice dai kakar zabe ga dimbin Maluma ya zamo lokacin hada-hadar neman abin Duniya, a yayin da wasu kuma ke siffatuwa da wannan siffa domin damfara, zamba tare da cuwa-cuwa tsakanin bayin ALLAH, ayayin da wasu kuma dake da wannan siffa ke bin ofisoshin manyan Jami’ai suna Maula da sunan Addini.

 

MUHALLI SHAHID.

 

Idan ana sanya rawani, rike kwagiri tare da tasbaha domin siffatuwa da siffa ta kamala, amma a gaza nesantar cin harumun din da zai munanta haduwar bawa da ALLAH, to yafi alkairi mutum ya dauki fartanya yaje yayi noma, ko Gatari yake yayi faskare, ko kuma Baro yaje yayi dako dan ya samu halalinsa, da mai yiwuwa hakan ya kyautata haduwarsa da ALLAH ya zamo abin soyuwarsa (Waliyi).

 

A TAKAICE DAI, ANA IYA SAMUN KUSANCI DA ALLAH, TA HANYAR NEMAN SANA’A KOMAI KANKANTARTA DA WAHALARTA TA HANYAR NEMAN HALALI, KUMA ANA IYA NESANTA DA ALLAH KO DA AN SIFFATTU DA SIFFA TA KAMALA AMMA IDAN YA ZAMO ANA CIN HARAMUN.

 

WALLAHU -A’ALAM.

 

NOTE: Wannan kawai fahimtace, mai yiwuwa sam shi ma’abocin rubutun ba haka yake nufi ba.

 

ALLAH YASA MU DACE. AMIIN YAA ALLAH.

 

Daga: Muhammadu Usman Gashua

Share

Back to top button