FATWA: Matsayan Shehu Ibrahim Niass RA, akan ɗiban kasar inda waliyyi ya taka ko shafar kabarin waliyyi.

Matsayan Shehu Ibrahim niass akan ɗiban kasar inda waliyyi ya taka ko shafar kabarin waliyyi ko taɓa rigar waliyyi.

 

A ranar farko da Shehu Ibrahim niass ya ziyarci garin Ibadan, manyan jiga-jigan malaman garin suka mai rakiya zuwa cikin gari, kuma aka dace ranar Jumu’a ne, sai suka ce Shehu yayi musu limancin Jumu’a, bayan an Kawo ruwa Shehu yayi alola sai wani majazubin Malami ya ɗibi ƙasan tafin kafan Sheh niass rta, Shehu bai ce komai ba sai bayan da ya gama limancin Sallah,

 

Sai shehu yayi tambaya wa ya ɗebi ƙasan tafin kafana ? Sai kowa ya razana sukayi shiru babu wanda ya iya bashi amsa, Shehu ya ƙara tambaya wa ya ɗibi ƙasan tafin ƙafana ?

 

Daga nan sai suka amsa mishi, sai Shehu ya ce manene dalilin ɗiban ƙasan tafin kafana ? Sai suka ce Shehu mun ɗiba ne domin neman tabaruki domin matsayinka na babban waliyin Allah, sai Shehu ya ce kasan tafin kafana ba zai sa ku samu tabaruki ba,

 

Saboda haka ɗiban kasan kafana ba zai ƙara wa mutum matsayi a wajen Allah ba, abin da zai ƙarawa mutum matsayi a wajen Allah shine shine koyi dani gurin Taqwa (Tsoron Allah).da aiki makamancin nawa.

 

Shehu ya ƙara da cewa mutumin da ke zama a ƙasar Senegal a Kaulaha inda nake amma bai jin tsoron Allah ba to yana nesa da ni kamar nisan gabas da yamma sannan mutumin da yake zaune a gabashin duniya ta inda rana ke hudowa idan yana jin tsoron Allah yafi kusa da ni fiye da kusancin da ke tsakanin harshe da lebe.

 

Allah yasa muna fahimtar saƙon ALLAH ya bamu albarkacin shehu. Amiin Yaa ALLAH

Back to top button