Garabasa Daga Manzon Allah SAW, Ayyukan Da Ake Gudanar Wa A Ranar Arfat.

NAFILAN DA AKEYI RANAR ARFAT TASAKANIN AZAFAR DA LA’ASAR CIKIN WANNAN RANA.

 

Annabi Muhammadu SAW, yace wanda yayi wannan sallan ranar Arfat tsakanin azafar da la’asar Allah zai rubuta maka ladan hasana miliyan (1) kuma Allah zai ɗaga a cikin Aljannah adadin harufan suran daka biya a cikin Sallar

 

Annabi Muhammadu SAW, yace tsakanin wannan darajan akwai tafiyan shekara (500) kuma Allah zai aura maka aure da hurul ini guda (70) adadin sura daka biya kuma kowace hurul ini a tare da ita akwai ma’ida ya ƙutu da dinare guda (100).

 

Kuma a cikin kowani ma’ida akwai nau’i nau’i naman tsintsaye guda dubu ɗari da saba’in masu sanyi da masu zaƙi kaman zuma ga ƙamshi kaman miski kuma wuta bata ƙonasu wuƙa bazata iya yankasu ba suna ɗanɗano mai daɗi.

 

Nafila ne raka’a (4) kowani raka’a fatiha 1 ƙulhuwallahu ahad ƙafa (50) duk raka’a biyu kai sallama.

 

Naji wasu suna cewa wai yin Azumi ranar juma’a ba kyau wlh ƙarya sukeyi saboda akwai hadisi cikin Bukhari da Muslim Ibn Majah duk sun tabbatar da cewa duk wanda yayi Azumi ranar juma’a Allah zai bashi ladan Azumin shekara dubu hamsin wannan falalan shike basu mamaki lallai basu san Allah ba sbd yanada ladan da ya wuce hankali sai dai imani kawai.

 

Allah yabamu ikon bauta mishi cikin ilimi ba cikin jahilci ba alfarman Ulumul Wara Annabi Muhammadu ﷺ (SAW).

 

RAUDHATUL HALILIT TIJJANIYA

08030461800

Share

Back to top button