Garin Tabuk Wanda Allah Ya Albarkaci Garin Da Kayan Lambu Saboda Addu’an Manzon Allah SAW.
Garin Tabuk yana daga cikin mu’ujjizan Manzon Allah Saww ﷺ.
Lokacin da Annabi ya tafi yaki sun tsaya a garin Tabuk wanda yake da ruwa kaɗan – sai ya wanke fuskarsa da hannayensa masu daraja sannan ya zuba ruwan a cikin kayan marmari sannan ya ce, ‘Ya Mu’azu, wataƙila idan ka yi tsawon rai, da sannu za ka ga wannan yanki cike da lambuna.
Albarkar Annabi Muhammadu Saww, a kwana a tashi a yanzu ana fitar da sama da wardi miliyan 20 a duk duniya daga Tabuk kowace shekara.
Bayan haka, garin cike yake da lambuna masu albarka, ƙasa mai albarka, da ‘ya’yan itatuwa da kayan marmari masu yawa. Tabuk yana daya daga cikin wuraren aikin gona a duk yankin kasar Saudi Arabia.
Allah ya kara masa soyayyan Manzon Allah Saww, ﷺ. Amiin Yaa ALLAH.
Daga: Babangida A. Maina