GASKIYAR MAGANA: Abunda Ya Faru Tsakanin Sheikh Munir Adam Koza Da Yaran Taka Lafiya

GASKIYAR ABINDA YA FARU.

 

Nayi bincike ta duk kafar da ta dace, karshe sai naci karo da batutuwa da kowa zai so jin amsar wadannan tambayoyin…!

 

1- Shin yaushe ne Sheikh Munir Adam Koza yayi wancan karatun…?

 

2- Shin me dalilin da ya sanyashi yin zancen?

 

3- Da gaske shi wanda yake keta alfarmarsa da yawun “ZAWIYYA MADAUKAKIYA TA SHEIKH MUHAMMAD NGIBRIMA” yake abinda yakeyi.

 

1- Shi dai wannan “Budeddiyar Nasiha” Sheikh Imam Munir yayine shekaru 2 da suka gabata, kenan ba karatun jiya bane ko kuma yau, kuma duk kalmonin da suka bayyana cikinta, to kalmomine da suka ginu a bisa waki’oin da suka wakana a wancan lokacin, saboda haka sam babu adalci a daukoshi a yanzu, kuma ya zamo abin kafa hujja ko yin hukunci, domin ko a kur’ani akwai ayoyin da sukan zamo tabbatattu da ababen sokewa gwargwadon abkuwar wata waki’ar bayan wata.

 

2- Sheikh Munir Adam Koza, yayi wannan karatune ba da niyyar batanci ko cin mutumcin kowa ba, face yayine domin da’a ga umarnin da mai Daraja, Sheikh Khalifa Fatihu (R.T.A) yayi ga masu wa’azi, a wani Mauludi da ya gabata, inda a bayyane ya fito yayi fatali da ababen soye-soyen zukata da matasa suka kir-kiro kuma suka addinantar wadanda dimbin barna suka yawaita cikinsu, kuma suka zamto suna kishiyantar abinda Darikar Tijjaniyya ta ginu akai a gefe guda kuma hakan ya zamo makami da makiya Darika da suke amfani dashi wajen yakar ‘yan Darika, inda shi Khalifa yayi umarni ga dukkan masu da’awa da su zage damtse wajen tashi su yaki wannan musiba.

 

3- Duk da kasancewar shi wanda yayi wannan cin fuska ga Imam Munir Adam Koza, ta hanyar dauko tsohon karatu tare da kafa hujja dashi ayau, ya kasance mai tsananta intisabi da Zawiyyar Maulanmu Sheikh Muhammad Ngibrima, to amma ALHAMDULILLAH, wannan Zawiyya ta bakin makusantanta masu girma, sun nesanta kansu ga wannan abin da ya aikata, hasalima su sun kasance suna tare 100% da hazikan Maluma matasa na Darikar Tijjaniyya cikin abinda sukeyi na ilmantarwa, fadakarwa da kuma bayar da kariya ga wannan Darika mai dimbin albarka.

 

Lallai babu shakka Mallam Rabi’u Taka Lafiya, yanayin Uslubin wakokinsa sun sauya daga yadda yake yinsu a baya, bal shima a halin yanzu ya kasance yana mai horo da a kiyaye shari’ah, da gujewa ketare iyakokin ALLAH, wanda hakan yake kara tabbatar da cewa shi wannan karatun ba na yanzu bane.

 

SABODA HAKA, DAN ALLAH MU GUJI BIJIRO DA ABINDA ZAI HAIFAR DA FITINA TSAKANIN YAN UWA, MU ZAMTO MASU AJE KOMAI A MAHALLINSA.

 

ALLAH YA KARFAFI WADANNAN HAZIKAN MALUMA MATASA AKAN ABINDA SUKEYI, YA BASU KARIYA DA KARIYARSA. Alhamdulillah

 

Daga: Muhammadu Usman Gashua

Share

Back to top button