GASKIYAR MAGANA; Farfesa Ibrahim Maqari Ya Fito Ya Bayyana Wa Duniya Gaskiyar Labarin Dake Cewa An Bashi Limanci A Makkah.

Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari Ya Fito Ya Bayyana Wa Duniya Cewa Labarin Da Ake Fada Akan Cewa An Basa Limancin Masallacin Makkah Ba Gaskiya Bale.

 

Shehin malamin wanda ya wallafa labarin a shafin sa na sada zumunta na Facebook inda ya bayyana cewa kamar haka;

 

Mutane suna ta kira akan wani labari da muka tashi dashi yau akan limancin masallachin Haram.

 

Ƙila dai fatan alkhairi ne ya sanya waɗanda suka ƙirƙiri labarin ƙirƙirarsa ko kuma sunaye ne suka yi kama.

 

Muna matuƙar godiya da dukkan kyawawan zato da fatan alkhairi daga masoya.

 

Wannan shine rubutun malamin daya wallafa a shafin sa na sada zumunta na Facebook, don haka muna kira ga duk wanda suka kirkiri wannan labarin dasu guji rubuta labarin da basu tabbatar da sahihancin da don tabbatar da ingantacen aikin jarida a ko’ina.

Share

Back to top button