Saboda Tsananin Kishin Sa Ga Manzon Allah SAW Yayi Shiga Halwa Na Tsawon Shekara Guda.

YA SHIGA HALWA TA SHEKARA GUDA SABODA KISHINSA AKAN YABON MANZON ALLAH (S.A.W).

 

Ya labarta yayin tattaunawarsa da Dan Jarida, cewa agarin da ya taso na Wudil, an kasance duk shekara ana gasa ta mawakan MANZON ALLAH (S.A.W) sai ya kasance an gama shirya gasa amma shi ba’a sanar dashi ba sai washe garin ranar da za’a gudanar dashi, kuma Maudu’in gasar shine “BAYAR DA TAARIHIN ANNABI (S.A.W) TUN DAGA HAIFUWA HAR ZUWA WAFATI A NAZAMANCE”.

 

Ko da akayi wannan gasa, mai-makon yazo na daya ko na biyu, sai sunansa ya fito na 7, saai aka dinga fadin wasu maganganu a gari wanda yayi matukar sosa masa zuciya.

 

Yaje gaban surar Shehu dake cikin dakinsa, sai ya lazimci niyyar shiga halwa akan ALLAH ya huwace masa baiwar da idan ya shata yabo, to har a nade kasa babu wani mai yin kwatankwacinsa a garin Wudil.

 

Ko ayayin da ya kammala wannan halwa, yana shirin fitowa cikin dare sai yayi mafarki da Sheikh Ibrahim Inyass (R.T.A) ya bayyana gareshi a siffa ta mai zuwa aikin Hajji, sai yace dashi “Umar dauko yabon da ka rubuta ka biyata muji” sai ya dauko a karkashin shifidarsa ya soma biya masa, ko da yazo kan wani baiti da yake cewa “ANNABI KANANAN TUN LOKACIN DA ALLAH BAI DA SUNA ALLAHU” sai Shehu yace dashi nan wajen yayi nauyi sosai, tashi daga wajen nan sauro yayi yawa, farkawarsa ke da wuya kawai sai ya samu dakin cike da sauro.

 

ABIN LURA.

 

1- Banda zallar kishin ANNABI (S.A.W) zunzurutun kaunar ANNABI (S.A.W) da kuma zallar sonsa, babu abinda zai kai Fada shigq Halwa har na Shekara guda, ta hanyar kauracewa dukkanin harkokinsa.

 

2- Halartowar Sheikh Ibrahim (R.T.A) garesa ALLAH ya nuna masa cewa ya karbi aikinsane, kuma shuhurarsa bazata zamo illa ba gareshi, domin an nuna masa cewa duk yadda zai hidimtu cikin soyayyar ANNABI (S.A.W) to akwai magabata a cikin hakan, sai ga Shehu ya bayyana gareshi domin daurashi a hanya, ba mamaki shi yasa ALLAH ya tseratar da Fadar Bege daga kudurtar kiyayyar wannan waliyi kamar yadda wancenansa suka kasance a haka.

 

MUNA KARA ROKAR MASA KARIN KUSANCI DA MANZON ALLAH (S.A.W) ALLAH YA NI’IMTA MAKWANCINSA. AMIIN

 

Daga: Muhammadu Usman Gashua.

Share

Back to top button