Gidauniyar Sheikh Ibrahim Maqari Ta Raba Kayan Abinci Ga Mabukata Don Bikin Maulidi

ALKAIRIN ALLAH, YARDARSA DA KUMA JIBANCINSA SU KARA TABBATA GA WANNAN BAWA NASA Prof. Ibrahim Maqari (H).

 

Akullum zukatanmu kara damfaruwa suke ga sonsa da kuma kaunarsa saboda ALLAH, saboda shi kam ya tattare dukkanin siffofi da dabi’u kyawawa, da suke sahhalewa zukata so da kaunar mutane kwatankwacinsa, soyayya mai cike da sallamawa.

 

Kwanaki 4 zuwa 5 da suka gabata, munje domin kai kayan tallafin abinci da Buhuna, ga wadanda Iftila’in ambaliya ya shafa a wasu kauyuka, wanda shi wannan bawan ALLAH ya jagoranci samarwa.

 

Ko ayau da na ga wasu idanuwa, da suka bukaci irin wannan tallafi a garin Gashua, amma suka rasa, anan na kara fahimtar tsadar irin abinda ya jagoranci samarwa ga al’ummun wadannan kauyuka.

 

Shidin ya kasance jagorane da yake wanzar da karantarwa a aikace.

 

ALLAH YA KARA MASA LAFIYA DA TSAWON KWANA, YA BUDE ZUKATAN WADANDA ALLAH YA BAIWA HALIN DA ZASU IYA TAIMAKAWA AL’UMMA SU ZO SU TALLAFA MUSU.

 

Muhammad Usman Gashua

Share

Back to top button