GUDANARWA DA MAULANA SHEIKH ALIYU JUMA’A MUHAMMAD RA, YA BAWA MUSULUNCI.
MUFTI: MAULANA SHEIKH ALIYU JUMA’A MUHAMMAD
A gidan da aka san darajar ilimi da tarbiyya da sanin ya kamata aka haifi Maulana Farfesa Sheikh Aliyu Juma’a Muhammad Abdulwahab Salim Abdullahi Salman, a garin Bani Suwaif a yankin da ake kira da “Sa’idu Misra” ranar 7 ga watan Maris, 1952, ya fara karatunsa tun yana ɗan shekara biyar a duniya, ya fara haddar Alkur’ani mai girma yana ɗan shekaru 10, ya kuma kammala haddarsa yana da shekaru 13, tun wancan lokacin mutum ne shi mai son karatu matuƙa, abin da ya ba shi daman faɗaɗa fahimta da gogewa wajen ta’amuli da ilmomi mabambanta..
Ya yi karatu a hannun manyan malamai, irinsu: Sheikh Muhammad Mahmud Farghaliy, da Sheikh Sayyid Saleh Awadh, da Sheikh Aliyu Ahmad Mar’iy, da Sheikh Ibrahim Abul Khashab..
Yana da wahala ka sami wani matani na ilimi a fannonin: Tajwidi da Hadisi, da Larabci, da Fiqhu da Gado, da Ƙira’at da Sheikh Aliyu Juma’a Muhammad bai haddace shi ba, ya kammala digiri na biyu a fannin “Usulul Fiqhi” a 1985, haka ma a fannin Usulul Fiqhi ya kammala digirinsa na uku a 1988.
Ijazozi kuwa da yake da suna da matuƙar yawa, a cikin waɗanda suka ba shi ijaza akwai:
– Sheikh Muhammad Abun Nur Zuhair, tsohon mataimakin shugaban jami’ar Al Azhar, malamin Usulul Fiqhi a tsangayar Shari’a, jami’ar Al Azhar, mamba a kwamitin bayar da fatawa, ya karantar da shi littafinsa mai suna “Usulul Fiqhi” duka mujalladi huɗu..
– Sheikh Jadur Rabbi Ramadhan Juma’a, tsohon shugaban tsangayar Shari’a da dokoki, jami’ar Al Azhar, shi ne ya yi wa Sheikh Aliyu Juma’a Muhammad laƙabi da “Imamus Shafi’iy ƙarami” saboda irin yanda ya kware a karatun da sani a mazhabar Imam al- Shafi’iy, a wurinsa ya karanci littafin “Fiqhus Shafi’iy” da “al- Ashbahu wan Naza’ir” na Imam al- Suyuɗiy.
Da sauransu..
Wasu daga cikin Muƙamai da ya riƙe sun haɗa da:
– Muftin Ƙasar Misra tun daga 2003 har zuwa 2013.
– Mamba a Majma’ul Buhus al- Islamiyya, da take ƙarƙashin Al Azhar Al Sharif tun daga 2004 har zuwa yau.
– Mamba a Majma’ul Fiqhi al Dauliy da yake ƙarƙashin ƙungiyar ƙasashen Musulmai, da ke Jidda, Saudiyya.
– Mamba a Mu’utamarul Fiqhil Islamiy, India.
– Mamba a kwamitin bayar da fatawa ta Al Azhar tun daga 1995..
Game da littattafan da ya rubuta kuwa, sai dai mu faɗi abin da ya samu, kaman:
1- المصطلح الأصولي والتطبيق على تعريف القياس.
2- الحكم الشرعي عند الأصوليين.
3- أثر ذهاب المحل في الحكم.
4- المدخل لدراسة المذاهب الفقهية الإسلامية.
5- علاقة أصول الفقه بالفلسفة.
6- مدى حجية الرؤيا.
7- النسخ عند الأصوليين.
8- الإجماع عند الأصوليين.
9- آليات الاجتهاد.
10- الإمام البخاري.
11- الإمام الشافعي ومدرسته الفقهية.
12- الأوامر والنواهي.
13- القياس عند الأصوليين.
14- تعارض الأقيسة.
15- قول الصحابي.
16- المكاييل والموازين.
17- الطريق إلى التراث.
18- الكلم الطيب.. فتاوى عصرية (جزآن).
19- الدين والحياة.. فتاوى معاصرة.
20- الجهاد في الإسلام.
21- شرح تعريف القياس.
22- البيان لما يشغل الأذهان مائة فتوى لرد أهم شبه الخارج ولم شمل الداخل. جزء أول ثم جزء ثان فيه حوالي مائة أخرى.
23- المرأة في الحضارة الإسلامية.
24- سمات العصر.. رؤية مهتم.
25- سيدنا محمد رسول الله للعالمين.
26- الفتوى ودار الإفتاء المصرية.
27- قضية تجديد أصول الفقه.
28- الكامن في الحضارة الإسلامية.
29- فتاوى الإمام محمد عبده (اعتنى به وقدَّم له).
30- حقائق الإسلام في مواجهة شبهات المشككين (بالاشتراك).
Ya jagoranci samar da Mausu’o’i masu yawa, kaman su:
1- الموسوعة الإسلامية العامة، صدرت عن المجلس الأعلى للشؤون الإسلامية.
2- الموسوعة القرآنية المتخصصة، صدرت عن المجلس الأعلى للشؤون الإسلامية.
3- موسوعة علوم الحديث، صدرت عن المجلس الأعلى للشؤون الإسلامية.
4- موسوعة أعلام الفكر الإسلامي، صدرت عن المجلس الأعلى للشؤون الإسلامية.
5- موسوعة الحضارة الإسلامية، صدرت عن المجلس الأعلى للشؤون الإسلامية.
6- موسوعة فتاوى ابن تيمية في المعاملات الإسلامية.
Bincike da maƙalu/ Ƙasidu:
1- الوقف فقهًا وواقعًا.
2- الرقابة الشرعية مشكلات وطرق تطويرها (بحث مقدم للمؤتمر الرابع لعلماء الهند).
3- الزكاة (بحث مقدم لمؤتمر علماء الهند الخامس).
4- حقوق الإنسان من خلال حقوق الأكوان في الإسلام (بحث لمؤسسة نايف).
5- النموذج المعرفي الإسلامي (بحث مقدم لندوة المنهجية بالأردن).
6- الإمام محمد عبده مُفتيًا.
7- التسامح الإسلامي.
8- الإسلام بين أعدائه وأدعيائه.
9- الإسلام يتفق ولا يصطدم ومبادئ السلام والعدل الدوليين.
10- النفس ومراتبها.
11- اقتراح عقد تمويل من خلال تكييف العملة الورقية كالفلوس في الفقه الإسلامي.
12- ضوابط التجديد الفقهي.
13- الكثير من المقالات الصحافية بالصحافة العربية والعالمية.
14- العديد من البرامج الإذاعية والتلفزيونية المصرية والعربية والعالمية.
15- العديد من المحاضرات العلمية في أكثر من 20 دولة.
16- خطب الجمعة مطبوعة في مجلد ومترجمة إلى الإنجليزية.
Tahƙiƙi:
• رياض الصالحين للإمام النووي، دار الكتاب اللبناني.
• جوهرة التوحيد للباجوري، (طبعة دار السلام).
• شرح ألفية السيرة للأجهوري، المجلس الأعلى للشؤون الإسلامية.
• الفروق للقرافي، (طبعة دار السلام).
• المقارنات التشريعية، لمخلوف المنياوي (مجلدان طبعة دار السلام).
• المقارنات التشريعية، لعبد الله حسين التيدي (4 مجلدات طبعة دار السلام).
• التجريد، للقدوري الحنفي (مجلدان طبعة دار السلام).
• الأحكام الشرعية في الأحوال الشخصية لمحمد قدري باشا (طبعة دار السلام).
• ينابيع الأحكام في معرفة الحلال والحرام لأبي عبد الله محمد بن زنكي الإسفراييني (المجلس الأعلى للشؤون الإسلامية).
• جمع الجوامع للإمام السيوطي، في الحديث النبوي (طبع بالاشتراك مع دولة الكويت).
Da dai sauransu, a yanzu shi ne shugaban kwamitin addini a majalisar wakilai ta ƙasar Misra.
Yana da ɗalibai masu yawa a faɗin duniya.. Allah ya ƙara masa lafiya da tsawon kwana masu albarka.. Amiin Yaa ALLAH