GUDUMUWAR DA SHEIKH IBRAHIM INYASS (RTA) YA BAIWA DUNIYAR MUSULUNCI.
GUDUMMOWAR DA SHEIKH IBRAHIM INYASS (RTA) YABAIWA DUNIYAR MUSULUNCI A TAKAICE
A Tarihin Karnin Da Muke Ciki, Bisa Kiyasi Da Ittifaki Tsakanin Musulmi Da Turawan Duniya, Babu Mutum Guda Daya, Wanda Duk Wani Fanni Da Ya Shafi Rayuwar Dan Adam Sai Da Ya Kasance Yayi Hidima Na Zarce Tsara Cikin Sa, Kuma Ya Cimma Nasara Abar Amfanuwa Da Yabawa Kamar Maulan Mu Sheikh Ibrahim Inyass (rta).
* KYAUTATUWAR TSATSON SA..
ALLAH Ya Zabar Masa, Mafi Kyaun Nasaba, Ya Zabar Masa Sunan Mahaifi Irin Sunan Mahaifin Sayyadina Rasulullahi (SAW) Wato Sayyadi Abdullahi (rta) Sannan Ya Zabar Wa Mahaifiyar Sa Itama, Suna Irin Sunan Mahaifiyar Sayyadina Rasulullahi (SAW) Wato Sayyida Aminatu (rta) Sannan Shi Kuma Sai ALLAH Ya Zabar Masa Suna Irin Sunan Kakan MANZON ALLAH (SAW) Wato Sayyadina Ibrahimu (AS) Sannan Sunan ‘Ya’ya Jikoki Da Sauran Zuriyar Sa, Sai ALLAH Ya Zabar Masa Kwatankwacin Sunayen ‘Ya’ya Da Jikokin MANZON ALLAH (SAW).
* ILMIN ADDINI.
Shehu Ya Kasance Malami Ne, Hazikin Gaske, Wanda ALLAH Ya Azurtashi Da Fasaha, Fahimta, Fikira, Falsafa, Da Kuma Kaifin Kwakwalwa Na Ban Mamaki, Bai Karatu Gaban Wani Malami Ba Koma Bayan Mahaifin Sa, Amma Sai Da Yazamo Gawutaccen Da Mashahuran Malaman Kasar Masar Suka Risina Ma, Tare Bashi Shedar Girma Suka Kirashi Da ” Sheikhul Islam”
Sannan Yakasance Masani Ga Nau’ukan Ilmin Addini Mabanbanta, Kamar Tafsiri, Hadisi, Fikihu, Lugga, Da Sauran Su, Kuma Yayi Talifai Cikin Mas’aloli Mabanbanta, Kuma Shi Ya Kasance Masanine Mai Zurfi Cikin Harkar Sufanci, Da Ilmin Ma’arifa, Da Shari’a Abar Kiyayewa,
Sannan Kuma Ya Yada Ilmi Ta Hanyoyi Mabanbanta Ga Musumai Wadanda Suke Cikin Garuruwan Duniya Mabanbanta..
* YAYE MAZAJE
Shehu Ya Yaye Almajiran Da Suka Zamo Jagorori A Duk Inda Suka Kasance Fadin Kasashen Duniya, Sannan Sun Kasance Ma’abota Basira Da Hazakar Ilmi, Da Harshen Su Ya Bambanta Da Harasan Wasu.
* ZAMAN LAFIYA
Shehu Ya Tallafa Da Bayar Da Gudummowa, Wajen Samar Da Yancin Kai Ga Kasashen Africa, Daga Mulkin Mallakar Turawan Yammacin Duniya, Ta Hanyar Wallafa Littafi Mai Sunan “Afrika Ta Yan Afrika Ce” Sannan Ya Taimaka Wajen Kawo Zaman Lafiya A Kasashe Dadama,
Wanda Dalilin Haka, Yazamo Ya Samu Lambobin Girmama A Kasashe Dadama Na Duniya,
YADA ADDININ MUSULUNCI.
Azamanin Rayuwar Sa, Shehu Yakan Shiga Birane Da Kauyuka, Harma Da Sauran Kasashe Da Nahiyoyin Duniya, Domin Aiki Na Da’awa Da Kiran Al’umma Zuwa Ga Addinin Musulunci, Shehu Ya Musuluntar Da Miliyoyin Mutane, Ciki Da Wajen Kasashen Nahiyar Africa.
SHIGA KUNGIYOYI DOMIN TALLAFAWA ADDINI.
Shehu Ya Shiga Kungiyoyi A Cikin Kasashen Duniya Dadama, Kama Daga Kasar Pakistan, Da Sauran Kasashe, Sannan Kuma Tare Dashi Aka Assasa Kungiyoyin Tallafawa Addini Irin Su Rabidatul Alami Al Islami Ta Kasar Saudiya, Sannan Kuma Shine Ya Zame Mata Mataimaki Na Farko.
SOYAYYAR MANZON ALLAH (SAW)
A Wannan Sha’ani, Shehu Ya Wassafa Talifai, Dadama, Sannan Kuma Ya Zurfafa Wajen Alkiblantar Da Dukkanin Al’amarin Sa Zuwa Soyayyar MANZON ALLAH (SAW) Sannan Ya Jadda Soyayyar Sahabban MANZON ALLAH (SAW) Ya Jaddada Soyayyar Iyalan Gidan MANZON ALLAH (SAW) Da Sauran Waliyai Baki Daya.
IRIN HIDIMA, ALKAIRAN DA SHEHU YA WANZAR A DUNIYAR MUSULUNCI BAZASU KIDIDDIGU BA, SANNAN KUMA BAZASU RUBUTU BA A WANNAN DAN MUHALLIN NA JERANTA HARUFFA KAYYADADDU.
FATAN MU DAI KULLUM SHINE, ALLAH YA KARA MANA SOYAYYAR SA, YABAMU IKON KOYI DASHI DAIDAI GWARGWADO, SANNAN YASADAMU DASHI A FADAR MANZON ALLAH (SAW) RANAR LAHIRA. AMEEEEEEEN