Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad Kauran Bauchi Yayi Muhimman Magagganu A Wurin Maulidi

Rayuwar Annabi SAW Ta Kasance Abar Koyi Tun Ma Kafin A Saukar Da Wahyi. Inji Gwamnan Jihar Bauchi.
“Tun kafin sauƙar masa da wahayi, rayuwar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ta kasance abar kwaikwayo ga ɗaukacin al’uma.
“Juriya, sadaukarwa, zaman lafiya, taimako da neman ilimi na cikin ababen da Manzon Allah ya koyar da sahabban sa masu daraja.
“Waɗannan da ma wasu na cikin kiran da nayi ga ɗaukacin al’umar musulmi da suka yi cincirindo daren jiya a filin wasa na tunawa da marigayi Firaminista Abubakar Tafawa Balewa a nan fadar jiha don taya mu bikin mauludin wannan shekara.
“A yau Lahadi da ake gudanar da zagaye a Bauchi da kewaye, ina kira ga al’uma da su gudanar da wannan biki cikin nutsuwa, lafiya da bin doka da oda alfarmar wanda muke bikin domin sa.
“Kada mu gajiya wajen kwaikwayon halayyen fiyayyen halitta tare da yawaita masa salati don neman sabati, yalwatuwar arziki da zaman lafiya ga jihar Bauchi da ƙasar mu Najeriya.
Allah ka cigaba da shiga lamuran mu alfarmar Annabi Muhammadu ɗan Amina”, cewar Gwamna Bala na jihar Bauchi.
Daga Lawal Mu’azu Bauchi
Mai taimakawa Gwamna Bala Mohammed
Kan harkokin Sabbin kafafun sadarwa