Hadisi Shine Zance Wanda Ya Iso Daga Wurin Annabi SAW Wanda Ba Wahayin Qur’ani Bane…

SAHIHIN HADISI A WURIN SUFAYE

 

A bisa tsarin ilimin zahiri na shari’ar musulunci, hadisi shine zance wanda ya iso daga wurin Annabi SAW wanda ba wahayin qur’ani bane, dauke da umurnin aiki ko hani ko nasiha ko wanin haka daga gareshi sallallahu alaihi wa sallam.

 

Hadisi yana zama ingantacce ne ta hanyoyin da aka samo shi daga wurin Annabi SAW, wato tabbacin ruwayar sa ta hanyar lura da kamalar wayanda suka ruwaito, tun daga kan sahabbai zuwa tabi’ai da sauran su.

 

Amma a wurin sufaye, hadisi yana zama ingantacce ne in har suka sadu da Annabi SAW cikin barci ko ido da ido ya sanar dasu ko suka tambaye shi akan hadisin da aka ruwaito daga gareshi kuma ya gaskata eh lallai haka ne.

 

Da yawa hadisan da zaka gani a litattafan sufaye, babu shi ko kuma ya sha banban da na sauran malaman zahiri wayanda suka farauto ilimin su daga littattafan magabata kawai babu saduwa da Annabi SAW. Shiyasa za kaga waliyi yace “Qala rasulillahi SAW …” babu an wane haddasana wane kaza da kaza, saboda direct daga Annabi ya samu wannan zancen babu wani a tsakani.

 

Duniyar musulunci ya samu dawwamammen tsarki ne saboda kasantuwar sufaye cikin kowani zamani.

 

Bayan wafatin Annabi SAW, an ruwaito wasu hadisai na qarya, an boye da yawa na gaskiya, anyi wa wasu ragi da qari, saboda son mulki ko kiyayya ga Addinin Allah, an kuma tilastawa magabata koyar da hakan ko kuma a bakin ransu, wasu sun yi, wasu sunyi shahada.

 

A yau, babu inda za kaje a sanar da kai haqiqanin saqon Allah da manzonsa tun daga tafsiri zuwa hadisi da fiqhu sai wurin ma’abota saduwa da Annabi SAW wato sufaye.

 

Nayi wannan rubutu ne saboda matasa masu shauqin neman ilimi musamman akan hadisi da fiqhu, toh kar ku rabu da tafarkin sufaye.

 

Akwai maganganu na addini da dama wanda in kaji shi, muddin kana da tsarkakakken imani, kasan akwai rashin ladabi ko kiyayya ko tawaya cikin sa ga addinin Allah.

 

Hankalin ku, jagoran ku!

 

Amma mu a sufanci, ba hankali ke mana jagora ba, hasken imani ne.

Sidi Sadauki

Back to top button