HADUWAR SAYYIDINA ALIYU (R.A) DA SAYYIDINA ABUBAKAR (R.A) A ‘KOFAR GIDAN ANNABI (S.A.W).

HADUWAR SAYYIDINA ALIYU (R.A) DA SAYYIDINA ABUBAKAR (R.A) A ‘KOFAR GIDAN ANNABI (S.A.W).

 

HIRAR TA BURGE NI MATUQA:

 

*. SAYYIDINA ALIY(R.A): Ya Kai Aminin MA’AIKI(S.A.W) Ai Tunda Mun Hadu a Dai Dai, Ba Zan Iya Shiga Gidan MA’AIKI(S.A.W) Ba, Sannan Kai Ka Biyo Bayana Ba, Don Haka Bissmillah.

 

*. SAYYIDINA ABUBAKAR(R.A): Ya Kai ‘Kanin MA’AIKI(S.A.W) Wane Ni Na Shiga Na Barka a Baya??? Bismillah.

 

*. SAYYIDINA ALIY: Ya Kai Wanda ALLAH Ya Aiko a Gaida Shi Ba Zan Iya Wucewa Ba.

 

*. SAYYIDINA ABUBAKAR: Ya Kai Wanda ALLAH Ya ‘Daura Aurensa Da Kansa Ba Zan Iya Wuce Ka Ba.

 

*. SAYYIDINA ALIY: Ya Kai Sirikin ANNABI(S.A.W) Ka Ja Gaba Na Bi Ka.

 

*. SAYYIDINA ABUBAKAR: Ya Kai Sirikin ANNABI Ja Gaba Na Bi Ka.

 

*. MALA’IKA JIBRILU: Ya RASULULLAHI! Ga Manyan Sahabban Ka Can Suna Muhawara Akan Wanda Zai Shiga Gaba, Su Kuma Mala’iku Nata Rubuta Masu Lada.

 

ANNABI MUHAMMADU(S.A.W) YANA ZUWA SAI YA RIQE HANNUNSU YA CE:

 

“MU SHIGA TARE… KUMA RANAR LAHIRA MA A HAKA ZA MU SHIGA ALJANNAH TARE”.

 

LA’ILAHA ILLALLAHU.

 

ALLAH YA BAMU ALBARKACINSU, YA KARE HARSHENMU DAGA CUTAR DA KOWANNE DAGA CIKINSU AMEEEN.

Share

Back to top button