HALACCIN YIN AZUMIN ARFA KODA YA FADA RANAR JUMA’A DA BAYANIN FALALAR YINSA.

HALACCIN YIN AZUMIN ARFA KODA YA FADA RANAR JUMA’A DA BAYANIN FALALAR YINSA

 

Sakamakon Ranar Arfa, a bana tayi daidai da Ranar JUMA’A Kamar irin Ranar Arfar da Annabi saww yayi Hajjin Bankwana a duniya.

 

An samu Wasu Mutane suna Magana a kan cewar Bai Halatta yin Azumin Afra a saboda don ya fada Juma’a, Kuma anyi Hani akan yin Azumin Nafila a RANAR Juma’a

 

To, Wannan ba sabo ne ba, ko Bakon Abu haka ya faru, Kuma tuni MALAMAN Musulunci a da da yanzu sun yi Magana da matsaya akan haka

 

1. Gaskiya ne, akwai Hadisi a Bukhari 1849 daga Abi Huraira RA yace yaji Annabi saww yace: Kar dayanku yayi Azumin Ranar JUMA’A sai idan zai yi Kafinta ko Bayanta (Alhhamis/Assabar)

 

2. A Muslim Hadisi 1930 daga Abu Huraira RA daga Annabi saww ya ce: Kada Ku ke6e Daren Juma’a da Kiyamullaili a cikin darare, Kuma Kar Ku ke6e Juma’a da Azumi daga cikin Ranaku sai idan yakasance daidai da Wani Azumi da dayanku ke YINSA

 

3 A Wadannan Hadisan ne, Wasu ke Ganin BAZA ayi Azumin Arfa ba idan ya fada Ranar JUMA’A, amma tun daga Karanta Hadisan idan an fahimta Za’a San ba, haka suke Nufi ba

 

4 Domin shi duk Wanda zai yi Azumin a Wannan Juma’a idan aka tambayeshi Azumin me yakeyi zai ce, Azumin Arfa, ba Azumin Juma’a da aka Hana ba, kawai Arfa ce, tayi daidai da Juma’a,

 

5 Kuma shekarar da Annabi saww yayi Hajjin Bankwana Basu San an ruwaito yace Kar ayi Azumin Arfa ba, ga Wadanda basuyi Hajji ba, tareda da ya fada Ranar JUMA’A

 

6 Sannan hanawar da akayi cewar Kar ayi, ba Hani ne, na Haramci ba, Hani ne na Karhanci, wato ko Juma’ar da aka ce, Kar ayi da nufin Azumin Juma’a, idan anyi Makruhi akayi ba haramun ba

 

7 Wannan shi ne Fahimtar Mai Sharhin Bukhari Ibn Hajar a cikin Fathul Bariy, da Ibn Qudama a cikin Almugniy da Annawawi a Sharhin Muhazzab da Ibn. Taimiya a Fatayi Kubra da Ibn Usaimin a Sharhin Almumtani’i har ma Addayibi a cikin Aunul Ma’abud yace Ittifaki ne

 

8 A cikin Malaman Mazhabobi kuwa da suka yarda cewar Za’ayi Azumin Arfa Koda ya fada Ranar JUMA’A, Domin Innamal A’amalu binniya sun hada da:

 

9 Imam Shafi’i, Ibn Hambal, Wasu cikin Mabiya Abi Hanifa, Kuma shi ne Fahimtar Wasu daga MALAMAN Salaf, kamar Ibn Qayyim da Shaukani da Asshijindiy da Wasunsu

 

10 Duk wadancan MALAMAN da Ibn Hajar da Fatawar MALAMAN Saudiyya da Misra, sun yi Ittifaki cewar da Hadisin ya Hana Azumin Juma’a, Wannan Bai shafi :

 

11 Wanda yayi Azumin tare da Alhamis ko Assabar ba, da Wanda yayi Azumin don yayi daidai da wata Rana da ya Sama Azuminta, kamar Mai Azumi yau Gobe ya Huta irin Azumin Annabi Daud AS

 

12 Ko Mai Azumin Rana Kebantatta kamar duk daya ga Kowane Wata ko KARSHEN wata ko tsakiya, Ko Azumi Arfa, ko Ashura, ko Alwashi, ko Azumin Ayyamul bidi da Azumi Ramuwa, da sauransu

 

Duk Wadannan Azumi Koda anyi Ranar JUMA’A to ba Haramci ba Karhanci Kuma Koda ITA kadai Juma’ar aka yi Azumin domin ba Niyyar Azumin Juma’a akayi ba, Azumin Wani Abu ne ya fado Juma’a kawai ko Assabar da sauransu

 

FALALAR AZUMIN ARFA (9) GA WATAN

 

Annabi saww yayi Bayani lokacinsa aka masa tambaya akan Falalar yin AZUMIN ARFA, yace Yana Kankare Zunubin Shekarar da ta wuce da Wadda zata kama ( Shekaru biyu kenan) yazo a Muslim daga Qatadat RA

 

Don haka Kada Rashin Fahimta taka ko ta Wani ta Hana ka samun Wannan Falalar Mai yawa bayan kuwa baka da tabbacin sake Ganin Arfar wata Shekarar

 

Kuma duk Wanda yayi Karatu, yasan cewar ba Juma’a, kawai ba har Assabar da Yamush sakki da Bayan aha’aban ya raba duka an Hana yin Azumin, amma Ittifaki MALAMAN Musulunci suka ce, Banda idan akwai Wani Dalilin yin haka kamar misalan da Muka kawo

 

Allah ne Masanin, Allah ya datar damu da duk abinda yake So yake yarda dashi, Allah ya bamu ikonyi ya kar6a mana, Ameen

 

Azumin Arfar zai Zama Juma’a ne 08/06/2022

Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau 1443AH

Share

Back to top button