Hassadar Dr. Sani Rijiyar Lemo Ga Shehu Ibrahim Inyass RA Duba Cikin Littafinsa.

Hassadar Dr. Sani Rijiyar Lemo Ga Shehu Ibrahim Inyass RA Duba Cikin Littafinsa:
هذه هي الفيضة، إنياس وآراءه في الميزان
Bayan da Dr. Sani yayi Tarihin Shehu R.T.A yayi bayani akan sukan Shehu na roƙar sa Matsayi da daƙar Addu’a da neman tsari da maƙiya wanda muka warware a Rubutun baya.
Sai ya shiga Bayani kan Zuwan Shehu Ibrahim Kano da yadda suka haɗu da Sarki Abdullahi a Hajji har ya nemi yazo ya ziyarci Kano har yazo a ziyarar Farko ziyarar Sirri kamar yadda Annabi S.A.W yayi da’awa a Sirri a farko sannan ya dawo ta Fili wacce ya kirawo mutane zuwa tafiyar sa ya kuma samu ƙabuli.
Adai-dai nan gun zaka ga Hassadar Dr. ta Fito fili inda yake jin haushi yadda Mutane suka karɓi Shehu da yadda suka dinga tabarruki da Abubuwan da Shehu yayi ta’ammali dasu kamar Shimfiɗa inda suke rarrabawa suna tafiya da ita gida, sai yace: wai lefin Malaman kano ne da suka Sallamawa Shehu suka zuga Jahilai saboda Muƙaman Ƙarya da suka bawa Shehu.
Kai kace ya manta yadda Sahabbai ke neman tabarruki da Kakin Annabi S.A.W da jininsa da gashinsa wanda Waliyyay da Malamai Magadan Annabawa ne don haka don an yiwa Shehu babu mamaki:
العلماء ورثة الأنبياء
ya bayyana ƙarara ga jama’a cewa Shehu Bawan Allah ne Waliyyi. kuma Daman yazo a Hadisi Ƙudsi ingatacce cewa Idan Allah yaso bawa yana saka Jibirilu da Sauran Mala’iku su soshi daga nan sai ya saka mai Ƙabuli kowa yaji yana sonsa.
إن الله إذا أحب عبدا نادى جبريل فقال: قد أحب فلانا فأحبه، فيحبه جبريل، ثم ينادي في السماء: إن الله قد أحب فلانا فأحبوه، فيحبه أهل السماء، ويوضع له القبول في أهل الأرض.
Wannan shine ya tabbata a Shehu Shehu ya samu ƙabuli, dukkan Sarakuna da Shugabannin Kano suka Sallamawa Shehu Sannan Dukkan Jigagan Malaman Kano suka Sallama kamar: Sheikh Tijjani Bin Uthman, Sheikh Atiku Sanka, Shehu Sani Kafinga Shehu Mai hula da dukkan Almajiransu.
Daga nan Sai Dr. Sani ya shiga Magana kan yadda a Ganinsa Waɗannan Shehunnan suka sami zamiya suka halaka cikin son Shehu da Kamba mashi ta yadda duk wanda be yarda dashi ba suke cewa ya fita daga Tijjaniyya a Mazhabar Shehu Mal. Tijjani. Ko ina ruwan Dr. Sani da wannan maganar shida ba Batijjane ba.
Daga nan sai ya kawo Wasu daga cikin Baitocin Shehunnan mu da yake ganin Shirka ne wanda bazance Dr. Besan Balaga ba amma duk wanda yayi Balaga yasan Majazi yasan cewa Maganagnu ne na Balaga da basa kusa da Shrika baitikan gasunan kamar balarabe ne yace:
أنت كأسد
Shin hakan na nuna lallai kai ɗin zaki ne, Allah yace:
كمشكوة فيها مصباح
Shin wannan tashbihin yaya mutum ze fassara shi, Shabbaha Hasken Allah da Alkuki me fitila, kawai Shehu yana nuna yana kwaikwayon Shehu ne a Sallah da Hajji da Azumi.
Sannan inma Shirka ne ko zamewa ne toh fah ba Shehu Mal. Tijjani Uthamn R.T.A ya fara ba Almajirin Ibn Taimiyya ne, ga ɗaya yana cewa Saman bakwai daga Ibn Taimiyya take, wani na cewa Ibn Taimiyya ne ruhinsa da sirrinsa da Aljannar sa duba screenshots a cikin:
العقود الدرية في مناقب شيخ الإسلام ابن تيمية
Sannan Babbar Hassadar da ta rufewa Dr. ido har yake ganin Naƙasu ne ace mutum ya samu kaɓuli agun wasu da ba ‘yan ƙasar ba a lokacin da yan ƙasar sa suka ƙishi. Wanda wannan ƙaramin Ɗalibin Sira yasan yadda Mutanen Makkah suka ƙishi suka guje shi suka kore shi ciki harda Baffan sa Abu Lahab, Amma hakan be hana Annabi S.A.W Ɗaukaka ba da ƙarfi ba wanda se da ya dawo ya zama shine a samansu, kamar yadda dai Shehu R.T.A aka wahalar dashi akaƙi shi a Senegal ya fito waje suka so shi kuma ya koma yanzu babu wanda zece Shehu da gidansa basu da tasiri a Senegal.
Sannan yayi maganar cewa wai Babu wanda ya fito yayiwa Shehu Inkari sai Mal. Abubakar Gumi inda ya zargi Shehu da bezo da komai ba sai Shirka da Munafunci, a lokacin da Gumin yake aikewa da Shehu Wasiƙa yana cemai Ɗalibinka ne wane kuma Shehu ya girmama shi har ya Umarci sauran Shehunnai dasu haɗakai dashi gun ƙarfafa Musulunci.
Yanzu Soyayyar Annabi S.A.W da bata ɓuya ga kowa ba itace Munafunci Agun gumi, ko kuma Jaddada Manhajin Zikiri da Salatin Annabi S.A.W da Istigfari shine Munafunci da Shirka koda yake tuni Sheriff Ibrahim Saleh ya gama da Gumi a wannan lokacin cikin littafin المغير da التكفير a Lokacin da Shehu Ɗahiru Bauchi ya hana shi sakat sai da ya zamo be isa yayi magana ba.
Daga: Sayyadi Ahmad Mukaddam