Hukumar Hisba Na Bauchi Ta Bawa Dr, Abdallah Gabon Kaya Daya Janye Kalaman Ka

Hukumar Hisba Na Bauchi Ta Bawa Dr, Abdallah Gabon Kaya Daya Janye Kalaman Ka:

 

An yi kira ga babban malamin addinin Musulunci Prof Abdallah gadon kaya da ya janye kalaman sa a kan jihar Bauchi

 

Shugaban hukumar Hisba na jihar Bauchi Barr Aminu Balarabe Isah yayi kira ga malamin addinin islama Dr, Abdallah Gabon Kaya daya janye kalaman sa na zargin Auren jinsi da wasu suke shiryawa a wani hotel dake garin Bauchi, inda malami yace wani mutun ne ya kira duk a waya ya fada masa shirin da akeyi na biyan wasu makuden kuɗin da aka biya don gabatar da wannan taro na masu auren jinsi.

 

Don haka shugaban hukumar Hisba a jihar Bauchi Brr Aminu Balarabe Isah ya fito ya bayyana kiran ga malamin na ya fito ya tabbatar da ikirarin sa ko ya janye kalaman sa.

 

Allah ya kare mu daga sharrin makiya. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button