IBRAHIM BN ADHAM (R.A), Wata Rana Yayi Tafiya Akan Hanyar Shi Sai Ya Had’u Da Wani Makiyayi.

Babban Waliyin Nan; IBRAHIM BN ADHAM (R.A), Wata Rana Yayi Tafiya Akan Hanyar Shi Sai Ya Had’u Da Wani Makiyayi. Ya Tambayi Makiyayin Nan Cewa:

 

*. Ibrahim Bn Adham(R.A) Ya Ce:”Shin Kana Da Wani Abin Sha a Tare Da Kai, Ruwa Ko Nono???

 

*. Makiyayi Ya Ce: Wanne Daga Ciki Kafi So???

 

*. Ibrahim Bn Adham(R.A) Ya Ce: Ruwa Nafi Bu’kata.

 

Sai Makiyayin Nan Ya ‘Dauki Sandarsa Ya Bugi Tandarkin Dutse Sai Ruwa Ya Ri’ka Kwarara Daga Cikin Wannan Dutsen, Sai Ya Sha Daga Gare Shi, Ruwan Nan Yafi ‘Kankara Sanyi Kuma Yafi Zuma Dad’i, Sai Sayyidi Ibrahima(R.A) Ya Tsaya Cak Cike Da Mamaki!.

 

*. Makiyayi Ya Ce: Ka Da Ka Yi Mamaki, Domin; IDAN BAWA YAYI BIYAYYA GA UBANGIJINSA KOMAI SHIMA SAI YAYI MASA BIYAYYA”.

 

ALLAH Ka Yarda Damu Kamar Yanda Ka Yarda Da Wannan Makiyayin, Ameeen.

Share

Back to top button