Idan Aka Sa Lura Siffar/Halittar ‘DAN ADAM Surarsa Aka Kwaikwaya Aka Ajiye Shi Ya Zama GWAMNATI. Inji Sheikh Dahiru Bauchi RA.

MAULANMU SHEHU TAHIRU USMAN BAUCHI (R.A) Yana Cewa:

 

“…Idan Aka Sa Lura Siffar/Halittar ‘DAN ADAM Surarsa Aka Kwaikwaya Aka Ajiye Shi Ya Zama GWAMNATI(A Duk Fadin Duniya),

 

MISALI…..

 

KWANYARSA(Kwakwalwarsa) Nanne ‘HEAD QUARTER’ Na Kowacce Gwamnati, Head-Quarter Ita Take Da Iko Da Duk Jiki(Gwamnati) Gaba ‘Daya,

 

Aikinta Ne Ya Sauko Zuwa ZUCIYA Nanne ‘OFISHIN SAKATAREN GWAMNATI’ Idan Huhu Ya Sheqo Numfashi Sai Zuciya Ta Tace,

 

Ta Fitar Da Mai Muni Ya Sake Shaqar Sabo, Jini Ya Biyo Ta Kwakwalwa Ya Bama Zuciya, Zuciya Ta Fesa Ma Jiki Gaba ‘Daya,

 

Sai CIKI(Tumbi) Nanne ‘CENTRAL BANK’, Idan Ya Kar6a Sai Ya Tace Sai Ya Rabama Sauran Rassan Ga6o6i Sai Su Ci Gaba Da Aiki,

 

Sai FARJI/AL’AURA Nanne MA’AIKATAN ASIRI ‘NATIONAL SECURITY’,

 

Sai IDO Yana Sa Ido Akan Abinda Zai Cuci Gwamnati ‘INTELLEGENT’ Kenan,

 

Sai KUNNUWA Suna Saurara Su Ji Abin Da Zai Cuci Gwamnati Su Sanar Da Ma’aikatan Asiri(Intellegent),

 

Sai HANNUWA Da ‘KAFAFU Nanne ‘Karfin Gwamnati Yake Wato Kamar Su; Sojoji ‘Yan Sanda, Alkalai, Gandurobobi, Immigration, Da Custom, Da Sauransu.

 

Mun Gode SHEHU(R.A)

 

ALLAH Ya Kara Lafiya Da Nisan Kwana MAULANA(R.A) AMIIN

Share

Back to top button