Idan Har ASUU Suka Janye Yajin Aiki, Sai Karatun Jami’a Ya Gagari Talakawan Nijeriya, Cewar Farfesa Umar Sani Fagge

Idan Har ASUU Suka Janye Yajin Aiki, Sai Karatun Jami’a Ya Gagari Kashi Tamanin Cikin Dari Na Talakawan Nijeriya, Cewar Farfesa Umar Sani Fagge

 

Daga Imam Indabawa Aliyu

 

Farfesa Umar Sani Fagge Malamin addinin musulunci a jihar Kano ya bayyana cewa yajin aikin da malaman jami’o’i a Najeriya ke yi suna yi ne don maslahar al’umma ba wai maslahar kansu ba.

 

Shaikh Fagge wanda malami ne mai tawadhu’u, zuhudu da tsoron Allah, a yayin karatun da ya saba gudanarwa, ya kalubalanci gwamnatin Najeriya cewa duk wata gwaninta da za ta yi ba za ta kai ta ilmi ba.

 

“Jama’a su wani wanda aka hana shi albashi sama da wata biyar ya hakura, in da maslahar malaman jami’a ce za su hakura su janye. Ina tabbatar wa da duniya maslahar Talakawa ce a ciki, wallahi idan suka janye da kyar kashi ashirin cikin dari na ‘ya’yan talakawa za su iya ci gaba da karatun jami’a. Sai dai Private, masu kudi ne kadai ‘ya’yansu za su yi karatu.

 

Duk abin da kuka sani a kasar nan gwamnati ta zare hannunta a ciki, kama daga lantarki, fetur da komai. Ilmin Primary da secondary ya karye na jami’an ne kawai a tsaye, shi kadai ne talaka ke daukan wani abu, mu da muke koyarwa a jami’an ne muka san bala’in da jami’a suke ciki, da wahala ka sami department din da ba wasu malaman ne ke haduwa su biya wa wasu daliban kudin makaranta ba, dubu talatin zuwa arba’in idan ka mayar da shi miliyan biyu waye zai iya biya?

 

Idan malaman jami’a suka janye, kowanne talaka sai ya biya sama da miliyan biyu. Don haka sai a yi addu’a don Allah ya haska wa gwamnatin ta gane lallai talaka ya kamata a cece shi a wannan lamari, duk inda gwamnati za ta zuba kudinta ba zai kai na wannan muhimmanci ba. Ilmi kamar gishiri ne idan ba kai ba miya, ilmi mai gyaran zamani. Idan babu shi ba inda kasar za ta je, kuma kullum gwamnati ita ce dakko wasu kwararru daga wasu kasashen ana barnatar da kudi.”

 

Inji Farfesa Sani Umar Fagge.

Share

Back to top button