Idan Kayi Sallah a Madina Kana Da Lada 1,000 In Kayi Sallah A Makka Kana Da Lada 100,000.

Wani ya tambayi Maulanmu Sheikh RTA cewan; Shin da Makka da Madina wanene Yafi?

 

Maulana Sheikh RTA yace masa: Idan kayi Sallah a Madina kana da lada 1,000 inkayi sallah a Makka kanada lada 100,000.

 

Abinda yasa abin yazama haka shine, wato shi Allah shike bada Lada Amman abakin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam akejin Farashin ladan, toshi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam saboda tawadi’unsa bayason ace yawan Lada yafi yawa a garinsa akan Garin Allah(SWT).

 

Amman idan bahakaba Mu’auna mana mugani;

Abu mafi tsada a Makka shine Baitullahi, Abu mafi tsada a madina kuma Rasulallahi, toshin da Rasulallahi Da Baitullahi wannene yafi???

 

Rasulallahi yafi komai Girma da Tsada acikin kayan Allah domin koda kiran Sallah ake bazakaji anacewa Ash’hadu anna Ka’aba Baitullahi Ba saidai kaji ance Ash’hadu anna Muhammadu Rasulallahi Sallallahu Alaihi Wasallam.

 

Saboda haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yafi Komai Duniya da Lahira, haka inda yakema yafi ko ina daraja.

 

Na’am Shehu

 

Allah kara lafiya da Tsawon Rai Yadawo mana daku lafiya albarkar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam A’min A’min.

Share

Back to top button