Idan Mutum Ya Rayu a Cikin Wani Lamari Har Ya Saba Da Shi, Lamarin Ya Kan Bi Jininsa(Ruhinsa) Har Ya Zama Shi.

IMAM HASSAN SHEIKH TAHIRU USMAN BAUCHI Ya Rubuta Cewa;

 

SHEIKH TAHIRU USMAN BAUCHI(R.A) Yana Cewa;

 

“Idan Mutum Ya Rayu a Cikin Wani Lamari Har Ya Saba Da Shi, Lamarin Ya Kan Bi Jininsa(Ruhinsa) Har Ya Zama Shi,

 

A Duk Lokacin Da Ya Ga Wadansu Mutanen Da Basu Saba Da Wannan Lamarin Na Shi Ba, Sai Zuciyarsa Ta’ki Kar6an Mutanen Sai Ya Ji Baya Sonsu”.

 

Na Ce; “A Kowace Magana Ta MAULANA SHEHI(R.A) Sai Ka-Ji ‘Kamshin Al-Qur’ani a Cikinta;

 

“قال معاذ الله أن نأخذ إلا من وجدنا متاعنا عنده إنا إذاً لظالمون”

 

ALLAH Ya ‘Kara Lafiya Da Nisan Kwana MAULANA SHEIKH(R.A), Ya Barmu Da SoyayyarKU(R.A) Da’iman. Amiin

Share

Back to top button