Idan Mutum Yayi Murna Da Samun Yancin Kai Yayi Sunna, Amman Idan Mutum Yayi Na Annabi SAW Yayi Bidi’a (Subhanallahi).

NIGERIA @62nd ANNIVERSARY

 

MAULANMU SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI(R.A) Yana Cewa;

 

“NIGERIA Ta Ware Wannan Rana (01 Ga Watan Oktoba) Don Tunawa Da Ranan Da Aka Samu ‘Yancin Kai Yau Fiye Da Shekaru Sittin,

 

Duk Randa Wannan Rana Ta Zagayo Sai An Shirya Bukukuwa a Ambaci Wasu Mutane Ayi Ta Yaba Musu a Bada Tarihinsu Ace Su Mutanen Kirki Ne,

 

Har Abada Kasa Bazata Manta Da Su Ba, Har Ma Wasunsu Ana Lika Hotunansu a Jikin Kudin Kasa Wai Don Dai Sun Sama Ma Kasa ‘Yanci,

 

To Jama’a Akwai Fa Wanda Ya Same Mu a Bakin Jahannama Za Mu Afka Ciki Ya Tseratar Da Mu Bai Barmu Ba Ya Kaimu Aljanna Kuma Shi Ne Wanda Ya Karba Ma Kowa ‘Yanci Duniya Da Lahira,

 

Shi Ne Mai Cetonmu a Filin Qiyama Ba Don Shi Ba Da Ba’a Yi Hisabi Ba, Shi ALLAH Yake Duba Ya Ji Tausayinmu Wato; ANNABI MUHAMMADU(S.A.W),

 

Don ALLAH Jama’a Akwai Wanda Ya Kamata a Kullum Ayi Murna Da Samuwarsa Irin ANNABI MUHAMMADU(S.A.W),

 

Ayi Ta Bada Tarihinsa Irinsa,

Ayita Bukukuwa Irinsa,

 

Ai Ba Wanda Ya Kawo Mana Alheri Irin ANNABI MUHAMMADU(S.A.W) Saboda Haka Shi Yafi Cancanta Ayi Ta Tunawa Da Shi Fiye Da Kowa”.

 

ALLAH Ya ‘Kara Mana ‘Kaunar SAYYIDUNA RASULULLAHI(S.A.W), Ya Bamu Albarkar Masu Albarka, Ya Zaunar Da Kasarmu NIGERIA Lafiya, Ya Yalwata Arzikinta, Don Alfarmar SHUGABA (S.A.W), Ameeen

Share

Back to top button