ILIMIN DARIKAR TIJJANIYA (Kashi Na Daya 1)

ILIMIN DARIKAR TIJJANIYA (Kashi na daya)

 

A’uzu billahi minash-shaɗanir rajim

Bismillahir Rahmanir Raheem

 

Nayi wannan rubutu ne dan yan’uwa su san Darikar Tijjaniya da abinda ta qunsa dan su fahimci abinda suke yi ba abun wasa bane.

 

1. WAYE SUFI?

 

Mutum ne musulmi Mumini Wanda Babu Abinda Yake Bukata A Duniya Sai Yardar Allah Da Neman Kusanci Da Manzon Allah SAW. Haka Kuma Baya Kwadayin Aljanna Ko Kuma Tsoron Jahannama, Yana Ibada Ne Dan Godiya Ga Allah Bisa Ni’imominsa Gareshi. Sufi Waliyyi Ne, Amma Ba Dukkan Waliyyi Bane Sufi.

 

2. MENENE SUFANTAKA?

 

Shine “Aikata Dukkan Abinda Allah Yakeso A Yadda Yakeso Ba Yadda Kakeso Ba, Da Barin Dukkan Abinda Allah Bayaso Koda Kai Kanaso Tareda Kyautata Zato Ga Allah Da Halittunsa.

 

3. MENENE DARIQUN SUFAYE?

Farko ƊARIQA Kalma ce Wacce Take Nufin “HANYA” Ko “TAFARKI” A Harshen larabci.

 

Darika a musulunci yana nufin tafarkin da za a bi dan Samun Kusanci da Allah da yardarsa cikin sauqi bisa qamun qafa da waliyan Allah.

 

Allah S.W.T shi yayi umurni garemu akan mubi tafarkin Sufaye inda yake cewa “Wattabi’i Sabila Man Anaba Ilayya” Wato Kubi Tafarkin Wanda Zai Taho Gareni.

 

Darikun Sufaye guda 313 Yana Da Tushe A Musulunci Kuma Hanyace Ta Samun Shiga Aljanna A Saukake. Annabi SAW Yace “Lallai Shari’ata (musulunci) Tazo Ne Bisa Dariku Guda 313, Duk Wanda Yayi Riko Da Ita (daya daga ciki) Ubangiji Zai Shigar Dashi Aljanna” (Dabarani ya ruwaito hadisin).

 

4. DARIKAR TIJJANIYA

 

Tijjaniya itace ɗarika ta qarshe a jerin Ɗariku guda 313 ɗin nan kuma Wanda Allah yaba ragamarta shine Sidi Ahmad bin Muhammad Attijaniy RTA. Cikakken Sharifi, shugaban waliyan Allah baki daya daga farkon duniya zuwa qarshe. Kuma shine cikamakin su baki daya. Annabi SAW ne ya bashi komai na darikar tijjaniya ido da ido ba a bacci ba.

 

5. ABINDA TA QUNSA DA HUJJOJI

 

Shehu Ibrahim RTA Yana Cewa: “Darikace Mai Tsantsar Falala Da Samun Yardar Allah Wanda Aka Gina Bisa Sunnar Annabi S.A.W Da Kur’ani”.

 

Darikar Tijjaniya Babu Komai A Cikinta Sai Abubuwa Guda Uku Kamar Haka:

A. ISTIGFARI: Allah Yana Cewa “Kayi Tasbihi Ka Godewa Allah Ka Nemi Gafararsa Lallai Shi Allah Mai Karbar Tuba Ne” (Suratun Nasri Aya Na 3). Duk Da Kasancewar Annabi SAW Wanda Baya Laifi Amma A Kullum Shima Yana Istigfari Sau 70 Inji Abu Huraira RA.

 

B. SALATIN ANNABI: Allah Yana Cewa “Lallai Allah Da Mala’ikunsa Suna Salati Ga Annabi SAW, Ya Ku Wayanda Kukayi Imani Kuyi Salati A Gareshi Da Aminci” (suratul ahzab aya na 56). Annabi SAW Yace “Mutanen Da Suka Fi Kowa A Wurina Sune Mutanen Da Suka Fi Yi Min Salati” tirmizi ya ruwaito shi.

 

C. LA ILAHA ILLALLAHU: Allah Yana Cewa “Ku Ambace Ni Zan Ambace Ku, Ku Gode Min Kar Ku Kafurce Min” Sannan Annabi SAW Yace “Mafificin Kalma Shine La Ilaha Illallahu”.

 

6. AYYUKANTA DA HUJJOJI

 

A. LAZUMIN SAFE DA YAMMA: Allah yana cewa “Kuma Ka Ambaci Ubangijinka Cikin Ranka Kana Mai Kaskantar Da Kai Da Nuna Tsoro Kuma Kana Mai Kas-Kas Da Murya Bada Karfi Ba, Safe Da Yamma Kada Ka Zama Mai Gafala” (Suratul A’araf Aya Na 205)

 

B. WAZIFA: Itace Hilakuz-Zikiri Wato Da’irar Zikiri. Anas RA Ya Ruwaito Cewa Annabi SAW Yace “Idan Kuka Zo Dausayin Aljanna Ku Tsaya Kuyi Kiwo A Ciki, Aka Tambaye Shi Ina Ne Dausayin Aljanna? Sai Yace Da’irar Zikiri” (tirmizi)

 

C. ZIKIRIN JUMA’A: Allah yana cewa “Sannan In Kuka Idar Da Sallah Sai Ku Watsu A Kasa Kuna Masu Nema Daga Falalar Allah Sannan Ku Ambaci Allah Ambato Mai Yawa Sai Ku Iya Tsira” (Suratul Juma’ati Aya Na 10.

 

SADAUKI NASIDI BASHIR ALFATAHIY

Share

Back to top button