ILIMIN TIJJANIYA (Kashi Na Biyu 3) Qa’idodinn Darikar Tijjaniyya

ILIMIN TIJJANIYA (kashi na biyu)

 

QA’IDOJIN DARIKAR TIJJANIYA

 

A’udhu Billahi minash-shaɗanir rajim

Bismillahir Rahmanir Rahim

Wa sallallahu alal fatihil khatimil Nasiril Hadiy wa alihi wa sahabihi haqqa qadrihi wa miqadarihil Azim.

 

7. QA’IDAR SHIGA DARIKA

 

Wayannan sune qa’idojin da suke wajibi ne mutum ya aminta dasu kafin ayi masa iznin shiga Ɗarikar Tijjaniya.

 

A. BA A DAINAWA IN AKA KARƁA.

 

Ma’ana in ka karɓa babu ranar da zakace kai ka gaji ko ka fasa dan haka ba zakayi lazumin da wazifar da zikirin juma’ar ba. Ba a gajiya, ba a fasawa ba a dainawa domin Alqawari ne. Alqawari kuwa abin tambaya ne kuma saɓata suffar munafukai ne.

 

B. BA A HAƊA TIJJANIYA DA WATA ƊARIKAR.

 

Wato kamar yadda naga wasu suna yi sai suce su QADIRAWA ne kuma TIJJANAWA ne. A’a sam ba a haɗa ta da wata ɗarikar. Shehu Tijjani a lokacin da Annabi SAW zai bashi wannan darikar, yana riqe da dariku kusan 40 akace amma Annabi SAW yace duk ya ajiye su ya riqi wannan shi kaɗai. Annabi yace masa NINE SHEHINKA NINE MAI YI MAKA MADADI.

 

C. BA A ZIYARTAR WANI WALIYYI WANDA BA BATIJJANE BANE DAN NEMAN ALBARKA.

 

Misali kaji ance waliyin Darika kaza yazo gari ko A’a Qabarinsa na wuri kaza bari kuje neman albarkarsa, A’a haka haramun ne. Amma kana iya zumunci da yan’uwanka wayanda suke wata darikar.

 

HUKUNCI

Duk wanda ya aikata daya daga cikin sharudda guda uku ɗin nan, ya yanke alaqarsa da tijjaniya sai in har ya sake komawa wurin muqaddami an sake yi masa izni.

 

8. QA’IDOJIN DAKE INGANTA AIKIN DARIKA.

 

Bayan ka karbi darika ka kiyaye sharuddan karbarta, toh lazumi da wazifa da zikirin juma’a akwai sharudda guda biyar akan su kamar haka

A. Niyya: dole kayi niyya yayin da zakayi lazumi ko wazifa ko zikirin juma’a.

 

B. Tsarkin Jiki: tsarkake jiki daga fitsari da bayan gida da maniyyi da sauransu

 

C. Tsarkin Tufafi: sanya tufafi masu tsarki ba wayanda shari’a ta haramta ba

 

D. Suturta Al’aura: Ba a yarda Batijjane ko Batijjaniya suyi lazumi ko wazifa ko zikirin juma’a da tsiraici a waje ba, dole namiji ya rufe cibiyarsa zuwa gwiwar sa, mace ta rufe dukkan jikin ta sai kawai hannayenta da sawayenta da fuska.

 

E. Rashin magana: yayin da kake lazumi ko wazifa ko zikirin juma’a, ba a son kayi magana da kowa sai dai in da larura waccw shari’a ta yarda da ita.

 

HUKUNCI

Duk wanda yayi watsi da ɗaya daga cikin sharuddan nan toh lazumin sa ko wazifarsa ko zikirin juma’ar sa ta lalace. Wajibi ne kuma ya sake yin su cikin kiyaye wayancan sharuddan.

 

9. QA’IDOJIN DAKE CIKA AIKIN BATIJJANE.

 

Idan ka kiyaye sharuɗɗa biyar din can na baya da suke iya rusa aikin ka, toh ga wasu masu ɗumbin yawa wayanda zasu sanya aikin naka ya zama karɓaɓɓe har ka samu abubuwan da ake samu na riba. Daga ciki akwai:

 

A. Fuskantar Alqibla yayin da zakayi lazumi (ko wazifa da zikirin juma’a in kai kaɗai ne ba a jam’i ba).

 

B. Zama irin na tahiya yayin wuridi. Wato zama da gefen ka na hagu ba zaman harɗe (zaman sarakuna) ba.

 

C. Da kiyaye salloli biyar cikin jam’i

 

D. Da biyayya ga iyaye da miji (ga matar aure)

 

E. Da aikata mai kyau da barin mara kyau

 

F. Da dawwama cikin son Shehu Tijjani so mai tsanani da son yan’uwanka tijjanawa.

 

G. Da yawan nasiha ga yan’uwa

 

H. Da hadarto surar Annabi SAW ko Shehu Tijjani ko shehinka yayin da kake wuridin tijjaniya.

 

I. Da kakkabe duniya da abinda ke cikinta daga zuciyar ka yayin da kake wuridin tijjaniya.

 

J. Da fahimtar ma’anar abinda kake fadi yayin wuridi.

 

Da sauransu…

 

QARIN BAYANI

1. Sharuɗɗa uku na farko su kaɗai suke iya fitar da mutum daga tijjaniya ba wani abu ba. Ballantana wani yayi maka barazana yace zai qwace darikar daga gareka in bakayi masa kaza da kaza ba. Saidai akwai manyan waliyai a cikin tijjaniya wayanda in ka taɓa su, tamkar ka taɓa Shehu Tijjani ne, taɓa Shehu Tijjani kuwa, yanke alaqa ne da tijjaniya. Wannan shi ake kira SALBU.

 

Watarana Shehu Dahiru Bauchi RTA yaje ziyara wurin Shehu Gibrima. Da ya juya zai wuce sai Shehu Gibrima yake cewa mutanen wurin, kunga wannan yaron? Nan gaba za a yiwa manyan shehunnai SALBU in suka taɓa shi.

 

Haka zalika Shan taba, Zina, ca-ca da sauran laifuka basa fitar da mutum daga tijjaniya amma babu kyau Batijjane ya aikata su.

 

2. Sharuɗɗa na biyu kuma su lalata aikin Batijjane suke yi.

 

3. Na uku kuma rashin aikata su baya lalata aikin Batijjane amma yana rage masa tibar aikin.

 

IN KAGA SUNNA A YAU HASKENTA NA ZAHRA, ZIKIRI SALATI SUNA JERANTUWA KU JIYA

 

TALLAHI KA GANSU SUNE SUNKA RAYA WAJEN, BAYAN MACEWASSA SHEKARU TILI KU BIYA

 

Daga: Balarabe Faruk

(Sadauki Nasidibashir Alfatahiy).

Share

Back to top button