ILLAR DA SOCIAL MEDIA TA YIWA HARKAR ILMI DA KARANTARWA.

ILLAR DA SOCIAL MEDIA TA YIWA HARKAR ILMI DA KARANTARWA.

 

Zamanin magabata, zaka samu manyan Malamai da suka amsa sunan Malumta, wasunsu ma sun wallafa tarin litattafai, da tarin mazaje, amma sun kasance sashensu na ziyartar Majalisai ko zaurukan ilmin sashensu, ba dan basu iya karanta larabci ba, ko dan ba su iya gane ma’anar abinda suka karanta ba, sai domin su dosani wani irin hasken fahimta da ALLAH ya adana a kirjin dayansu, kuma kowanne guda na girmama dan uwansa.

 

Amma zamanin da muke ciki, kai fa daga yadda ake hada baki da kiran kalmomin larabcin wadanda ke nada kawunansu a matsayin Malamai, kasan akwai matsala, domin basu ma karantawa dai-dai, balle aje ga batun fahimtar abinda sakon ya kunsa dai-dai, amma a hakan suke daukar kuskuren da jahilcinsu yayi musu silar fahimtarsa a yadda suka fahimceshi, a matsayin hujja ko makamin yaqar wasu da suke da mummunan kuduri kansu, wanda kuma zaka samu zancen wanda suke son yaka, wani Mashahurin Malami ne da duniyar ilmi ta jinjinawa ilmi da fahimtarsa ga addinin ALLAH.

 

Lallai Media ta zo da alkairai dayawa, amma sharrinta ta fuskar abinda ya shafi ilmi da karantarwa yafi amfaninsa yawa.

 

ALLAH YA KUBUTAR DA MU DA YAN BAYA DAGA MAKIRCIN MALAMAN ZAMANI. ALHAMDULILLAH.

Share

Back to top button