ILMI A WURIN SUFAYE: Karɓi Darikar Tijjaniya Sannan Kayi Azkarun Tarbiyya Dan Kasami Tsarkin Zuciya Ka Shiga Sahun Masu Kyakkyawar Niyya.
ILIMI A WURIN SUFAYE.
Da Sunan Allah Al’Aleemu Al’Hakimu, Dubun Salati ga mai Qadari Al’azeemu, da Alihi da sahabbai Ahlil kiramu, da Shehu Ahmad Tijjani Khatimi Al’imamu, da Alhaji dan Alhaji maulaya sayyadi Barhamu, Da Ahmadu ɗan Aliyu jinin Karima da Kareemu.
Haqiqa Ilimi shine jagoran dukkan ayyuka. Dan haka Allah yayi umurnin a nemi ilimin sanin sa kafin a bauta masa kuma Annabi SAW ya wajabta neman ilimi wurin musulmi babba da yaro.
Kalmar ILIMI asalinta daga larabci ne kuma tana nufin SANI (knowledge). Ilimi shine sanin ya kamata da rashin ya kamata da kuma yaya abu kaza yake ya ake bi dashi.
Ilimi a wurin musulmai AMMAWA yana nufin sanin Allah da ilimin yi masa bauta na farilla.
Wajibine Musulmi yasan Allah ta halittun shi masu ban mamaki kamar rana da wata da sammai ba tareda an tokare su ba da wayewar gari bayan dare yayi da fitowar shuka daga cikin qasa da Teku da manyan tsaunuka da sauransu. Sannan Wajibi ne musulmi ya san abubuwan da suka rataya a kanshi na ibada a yadda zaiyi su da lokutan yinsu da tsare tsaren su.
Baya wannan, duk abinda musulmi ya samu na ilimi, toh ba wajibi bane a kansa kawai dai ya qara samun hasken rayuwa ne daga falalar Allah kamar yadda yazo “Idan Allah yana nufin bawa da rahma, sai ya bashi zurfin ilimi a addini”
ILIMI A WURIN SUFAYE
Farko dai kalmar ilimi tana da haruffa guda uku kamar haka علم
ع- على
ل- لوح
م- محفوظ
ALA LAUHUL MAHFUZ
Wato Ilimi yana tattare ne a lauhul Mahfuz!
ILIMI ya rabu kashi biyu, akwai SHARI’A akwai HAQIQA. kowannen su yana da fanni guda goma 12. Ba zaka zama masanin shari’a ko haqiqa cikakke ba sai ka san kowani fanni.
Sufaye sun raba fannoni Sha biyu-biyun nan gida hudu kamar haka
1. Ilimin Zahirin Shari’a
2. Ilimin baɗinin Shari’a
3. Ilimin baɗinin baɗini (ma’arifa)
4. Ilimin Haqiqa.
Suka ce dukkan ilimin nan suna cikin Al’qur’ani mai girma. A ciki ake samun su duka.
Hujjar su kuwa itace: Wanda aka saukarwa Al’qur’ani baki dayanta bai iya rubutu ba bai iya karatu ba, amma yafi kowa ilimi da sanin ma kana wama sayakuna. Har Allah yana cewa duk abinda ya fadi mune muka faɗa.
Menene sirrin ilimin nan nasa?
A lokacin da Jibrilu A.S yace masa IQRA’A! Sai Annabi SAW yace masa ni ba mai karatu bane, ya ce masa IQRA’A a karo na biyu yace masa ni ba mai karatu bane. A karo na uku yace masa IQRA’A BI’ISMI RABBIKA nan take Annabi SAW ya fara zubo masa karatu. Daga ina ilimin yazo alhalin bai karanta ba? Kar kuyi mamaki, Allah yana cewa WA ALLAMNAHU MIN LADUNNA ILMA wato Kuma muka sanar dashi ilimi daga garemu.
Wannan yasa sufaye basa damuwa da ilimi tunda baki dayanta a allo take, ashe kuwa Allon ya fita girma, toh yaya girman mahaliccin Allon yake?
Da suka kwaɗaitu da samun falala irin na shugabansu SAW. Sai Allah ya basu amsa yace WATTAQULLAH WA YU’ALLIMU KUMULLAH “Kuji tsoron Allah sai Allah ya sanar daku ilimi”
Sirrin ILIMI shine TAQWA
Dan haka sufaye suke cewa HARAMUN NE MUTUM YAJE NEMAN ILIMI DAN YA ZAMA MALAMI MAI BAYAR DA DARASU.
Amfanin Ilimi, aiki dashi, aiki da ilimi kuwa shine TAQ-WA ba wani abu ba. A sameka da ganin Girman Allah a cikin komai a ko ina.
Dan haka tarin ilimin littafi wato qur’ani da hadisi ba tareda samarwa Allah mazauni a zuciya ba, ba zaka taɓa samun ilimi mai albarka ba. Imam Maliku RTA yace “Mai ilimin Qur’ani da hadisi kawai, fasiqi ne. mai ilimi Haqiqa kawai, ziddiqi ne. Amma wanda yake da shari’a da Haqiqa shine masanin Allah mai babban rabo tabbatacciya”
Mai Ahalari yana cewa “Abin farko da ya wajaba a kan baligi shine INGANTA IMANINSA. wato bayan ka yarda da Allah, toh wajibi ne ka samawa Allah wurin zama a zuciyarka kafin ka nemi ilimin sanin ya zaka bauta masa.
Shehu Ibrahim RTA yace “Duk wanda bai san Allah Ar-rahman ba, ya taɓar da rayuwarsa tsawon zaman”. Koda Shekarun sa dubu da haddar litattafai dubu sau dubu, yayi asara muddin bai samu TAQ-WA ba.
TAQ-WA bata samuwa sai da tsarkin zuciya, tsarkin zuciya bata samu sai da riqo da waliyi masanin illolin zuciya.
Karɓi Darikar Tijjaniya sannan Kayi Azkarun Tarbiyya dan kasami Tsarkin Zuciya ka shiga sahun masu Kyakkyawar Niyya.
Daga: Sir Sadauki