IMAM AL-GHAZALI (R.A) Yace:”Dole Ne a Kame Ga Barin Ka@firta Duk Wani Musulmi, Komin Sa6anin Ku

HATSARIN KAFIR@TA DAN’UWAN MU MUSULMI.

IMAM AL-GHAZALI (R.A) Ya Ce:”Dole Ne a Kame Ga Barin Ka@firta Duk Wani Musulmi, Komin Sa6ani, Matukar Yana Riko Da Kalmar; “La’Ilaha IllalLahu Muhammadur RasululLahi” Cikin Gaskiya, Ba Kuma Tare Da Ya Warware Ta Ba, Saboda Akwai Babban Hatsari a Tare Da Kafirta Musulmi, Shi Kuwa Yin Shiru Game Da Hakan Ba Shi Da Hatsari, Yin Gaggawar Ka#firta Musulmi ‘Dabi’a Ce Da Take Tattare Da Wadanda Jahilci Ya Yi Masu Yawa..

 

Ku Sani Cewa Yin Kuskure Wajen Barin Kafirai Dubu(1000), Ya Fi Sauki Akan Zubar Da Jinin Musulmi ‘Daya…..” ~ [Adhwa’un Alaa Al-Maukifush Shi’iy Minas Ashabir Rasul, Shafi Na: 10].

 

Malamai Sun Bayyana Cewa; Babu Yanda Za’a Yi a Ka@firta Musulmi Saboda Wani Laifi Da Ya Aikata Na Zunubi, Wannan Yana Cikin Asalin Akida a Wurin Musulmai, Ko Da Kuwa Zunubin Da Ya Aikata ‘Din Yana Cikin Manyan Zunubai – Muddin Ba Shirka Ba Ne, ALLAH Madaukakin Sarki Yana Cewa:

“Lallai ALLAH Ba Ya Gafartawa Wanda Ya Hada Shi Da Wani a Wajen Bauta, Sai Dai Yana Gafarta Abin Da Bai Kai Haka Ba, Shi Ma Ga Wanda Ya So, Duk Wanda Ya Hada ALLAH Da Wani a Wajen Bauta, To Kuwa Lallai Ya Aikata Babban Laifi”, ~ [An-Nisa’i: 48],

Kai Ma Malamai Ba Sa ‘Daura Kalmar Kafirci Akan Wanda Ya Aikata Shirka, Su Kan Dai Ce Masa; ‘FA@SIQI’, Ko Kuma Ya Sami Tawaya a Cikin Imaninsa, Muddin Dai Ba Ya Halatta Yin Shirkar Ba Ne; Saboda Shi Asalin Ka@firci Shi Ne; ‘Ka@ryata Abin Da Aka Yi Imani Da Shi Da Gangan, Da Kuma Jin Cewa Hakan Ne Dai Dai Har a Cikin Zuciyarsa, Ya Kuma Natsu Da Haka, Domin Kaman Yanda Imani Yake a Matsayin I’itikadi, Haka Shi Ma Ka$firci I’itikadi Ne, Ma’ana a Zuciya Suke;”Lallai Fushin ALLAH Yana Kan Wadanda Suke Furta Maganganu Na Kafir$ci Bayan Sun Riga Sun Yi Imani, Sai Dai Wanda Aka Tilasta Masa Furta Kalmar Ka@fircin, Alhalin Kuwa Zuciyarsa Ta Gama Natsuwa Da Imani Da ALLAH, To Wannan Kam Ba Shi Cikin Fushin ALLAH…..” ~ [An-Nahli: 106].

Saboda Haka, Ko Menene Musulmi Zai Aikata Na Sa6o, Ba Zai Ka#firta Ba, Matukar Ba Yana Ganin Halaccin Abin Da Ya Aikatan Ba Ne, Amma Dai Imaninsa Zai Ragu Ya Sami Tawaya.

Saboda Haka Ne IMAM AL-GHAZALI(R.A) Yake Cewa:“Asalin Abin Da Ake Ka#firta Musulmi Da Shi Wanda Babu Wani Kokwanto Akai Shi Ne: Duk Wanda Ya ‘Karyata ANNABI MUHAMMADU (SallalLahu AlaiHi Wa Sallam), To Kuwa Lallai Kafiri Ne Shi”. ~ [Al-Iktisad Fil I’itikad, Shafi Na: 134].

Via By Sayyadi Othman Muhammad.

ALLAH Ya Bamu Ikon Kiyayewa, Ya Qara Tsare Mana Imaninmu Ameeeeeen.

Share

Back to top button