Imam Bukhari Ya Zaman Babban Mashahurin Malami Masani Wanda Duniyar Musulunci Ta Karbe.

Da yawa daga cikinmu mun ji labarin Imam Bukhari amma ba da yawa daga cikinmu ba ne suka san haka game da rayuwarsa.

 

Lokacin yana karami ya yi rashin lafiya sosai har ya rasa ganinsa gaba daya ya zama makaho. Mahaifiyar Imamul Bukhari ta riga ta rasa mijinta jim kadan bayan an haifi danta wato Imam Bukhari.

 

Wata rana da daddare mahaifiyar Imam ta yi kuka har bacci ya kwashe ta. Me ya faru a wannan daren ? Sai Ta ga Annabi Ibrahim a cikin mafarkinta ya ce mata, ‘Allah ya mayar da ganin yaronki gare shi saboda kuka da addu’o’inki.’ Da safe ta farka, ta ga yaronta ya warke sarai.

 

Imam Bukhari ya zama babban mashahurin malami masani wanda duniyar Musulunci ta karbe shi a wannan zamanin.

 

Allah ya karbi shahadar sa, ya bamu albarkacin Imam Bukhari da sauran waliyai bayin Allah. Amiin

Share

Back to top button