IMAMU AL-FAZAZEE (R.A) Yana Yabon Sahabbai a Gwala-Gwalan Baitotinsa Inda Yake Cewa.

IMAMU AL-FAZAZEE(R.A) Yana Yabon Sahabbai a Gwala-Gwalan Baitotinsa Inda Yake Cewa:

 

أولو البر والتقوي وأهل الفضائل

 

“Su Sahabbai Ma’abota Alkhairi Ne Da Nagarta Da Tsoron ALLAH Da Falaloli Ne”,

 

عصابة إشفاق وخير ونائل

 

“Jama’a Ne Masu Tausayi Da Alfahari Da Baiwa Da Kyauta”,

 

سمت بقبول الحق من خير قائل

 

“Su Fa Sun Daukaka Ne Ta Hanyar Karbar Gaskiya Daga Mafi Alherin Masu Magana (S.A.W)”,

 

أقرت لأيات له ودلائل

 

“Sun Tsaya ‘Kyam Gare Shi Ne, Saboda Ayoyi Da Hujjojinsa Da Su Ka Tabbata”

 

بها الصبح طلق والطريق موطأ

 

“Garai-Garai Suke Kuma Hanyarsu (Hanyar) Bi Ce!”.

 

ALLAH YA ‘KARA DADIN TSIRA DA YARDA GA SAHABBAN MANZON ALLAH(S.A.W) YA BAMU ALBARKARSU, AMEEEEN

Share

Back to top button