“Ina mamakin, mutumin da yake cikin tsoro amma bai dukufa cikin karanta “HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKEEL” Ba.

ADDUA ITACE MAKAMIN MUMINI

 

“Ina mamakin, mutumin da yake cikin tsoro amma bai dukufa cikin karanta “HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKEEL” ba.

 

Ina mamakin mutumin da Bakin ciki ya dame shi amma bai karanta “LA ILAHA ILLA ANTA SUB’HANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZALIMEENA” ba.

 

“Ina mamakin Mutumin da Masu Makirci suka dame shi da Makirci amma bai karanta “WA UFAWWIDHU AMREE ILAL LAAH. INNAL LAAHA BASEERUN BIL ‘IBAADI’ ba”.

 

“Ina mamakin mutumin da yake fama da wata jinya ko rashin lafiya, amma bai yawaita karanta “RABBI ANNEE MASSANIYADH DHURRU WA ANTA ARHAMUR RAHIMEENA’ ba”.

 

“Ina mamakin mutumin da yake neman haihuwa amma bai yawaita “RABBEE HABLEE MIN LADUNKA DHURRIYYATAN TAYYIBAH, INNAKA SAMI’UD DU’A’I ba”.

 

“Ina mamakin mutumin da talauci ya dame shi amma bai yawaita Istighfari da Salatin ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA ba.

 

Ina mamakin mutumin da ya shiga matsala amma bai yawaita LA HAULA WALA ƘQUWWATA ILLA BILLAHIL ‘ALIYYIL ‘AZEEM ba

 

Allah Ya Sa Mu Dace Albarkan ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA. Amiin

Share

Back to top button